Arsenal ta tsawaita kwantiragin Tomiyasu zuwa karshen 2026

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan Arsenal, Takehiro Tomiyasu ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Emiearte zuwa kaka biyu.
Tun farko kunshin kwantiragin dan kwallon Japan zai kare a karshen kakar bana, amma yanzu zai ci gaba da wasa zuwa karshen kakar 2026.
Tomiyasu ya buga wa Gunners karawa 73 a dukkan fafatawa tun bayan da ya koma Emirates daga Bologna a 2021.
Mai tsaron bayan ya yi wa Gunners wasa 20 a dukkan karawa a bana da cin kwallon farko a fafatawar da Arsenal ta caskara Sheffield United 5-0 a Premier League cikin Oktoba.
Arsenal tana ta daya a kan teburin Premier League da maki 46, iri daya da na Liverpool ta biyu, kuma saura wasa 10 ta kare kakar bana.
Rabon da Arsenal ta dauki babban kofin tamaula na Ingila tun 2004, wadda ta kai kwata fainals a Champions League na bana.
Za ta fafata da Bayern Munich gida da waje a cikin watan Afirilu.





