Arsenal ta koma ta daya a Premier bayan casa Forest

An wallafa

Arsenal ta yi nasarar casa Nottingham Forest da ci 5-0 a wasan mako na 14 a gasar Premier League ranar Lahadi a Emirates.

Gunners ta ci kwallon farko ta hannun Gabriel Martinelli a minti na biyar da fara wasan, haka suka je hutun rabin lokaci.

Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne Arsenal ta kara hudu ta hannun Reiss Nelso da Reiss Nelson da Thomas Partey da kuma Martin Odegaard.

Da wannan sakamakon Gunners ta koma matakinta na daya a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 31, bayan karawa 12.

Manchester City ta koma ta biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da Gunners, wadda itama ta yi fafatawa 12 a gasar Premier ta kakar nan.

Wannan shi ne karo na 19 da Arsenal ta ci kwallo biyar ko fiye da haka a Premier League, yayin da 18 daga ciki a karkashin Arsene Wenger aka yi bajintar.

Arsenal za ta buga wasan mako na 15 ranar 6 ga watan Nuwamba, inda za ta kara da Chelsea a Stamford Bridge a gasar Premier League.