Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Haaland ya karasa fitar da Bayern a Champions a Jamus
Manchester City da Bayern Munich sun tashi 1-1 a wasa na biyu a zagayen quarter finals a Champions League ranar Laraba a Jamus.
City ta ci kwallon ta hannun Erling Haaland a minti na 12 da komawa zagaye na biyu a Allianze Arena.
Kwallo na 12 da ya zura a raga a Champions League a bana, shine na daya a yawan cin kwallaye a gasar a kakar nan.
Haaland ya yi kan-kan-kan da Ruud van Nistelrooy dan wasan Premier League da ya ci kwallo 12 a Champions League a kakar 2002/03.
Haka kuma tun farko Haaland ya barar da fenariti a wasan na ranar Laraba, karon farko daga 16 da ya buga a baya, tun bayan da ya barar a Borussia Dortmund da Union Berlin a Afirilun 2021.
Saura minti takwas a tashi daga wasan Bayern ta zare daya ta hannun Joshua Kimmich a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Da wannan sakamakon City ta kai zagayen daf da karshe da cin kwallo 4-1 gida da waje ta fitar da Bayern daga gasar bana.
Pep Guardiola ya zama na uku da ya ci wasa na 100 a Champions League a matakin koci, wanda ya ja ragamar Barcelona da Bayern Municyh da yanzu a City.
Bayern Munich ta yi canji biyu ko ta sauya sakamakon, inda Sadio Mane ya canji Leroy Sane, wadanda suka tafa hannu.
Ranar 11 ga watan Afirilu a Eihad, bayan da aka ci Bayern 3-0 an bai wa hammata iska tsakanin Mane da Sane, inda wasu rahotanni suka ce dan wasan Senegal ya naushi Sane.
Daya canjin da Bayern ta yi a lokaci guda shine wanda Joao Cancelo ya maye gurbin Alphonso Davies.
Wannan shine karon farko da aka tashi 1-1 tsakain kungoyin biyu, inda City ta yi nasara a hudu, Bayern Munich ta ci wasa uku daga takwas da suka kara a Champions League.
Wasa takwas tsakanin Bayern da Manchester City:
Champions League Laraba 11 ga watan Maris
- B Munich 1 - 1 Man City
Champions League Talata 11 ga watan Afirilu
- Man City 3 - 0 B Munich
Champions League Talata 25 ga watan Nuwambar 2014
- Man City 3 - 2 B Munich
Champions League Laraba 17 ga watan Satumbar 2014
- B Munich 1 - 0 Man City
Champions League Tu 10Dec 2013
- B Munich 2 - 3 Man City
Champions League We 02Oct 2013
- Man City 1 - 3 B Munich
Champions League We 07Dec 2011
- Man City 2 - 0 B Munich
Champions League Tu 27Sep 2011
- B Munich 2 - 0 Man City
Manchester City ta zama ta uku daga Ingila da ta kai daf da karshe a kaka uku a jere a Champions League idan ka hada da Chelsea da Manchester United.
Da wannan sakamakon Real Madrid za ta karbi bakuncin City a karawar daf da karshe ranar 10 ga watan Mayu a Santiago Bernabeu.
Wasa na biyu kuwa a City za ta yi ne ranar 15 ga watan Mayu - Real ce ta fitar da Manchester City a daf da karshe a bara.
Real Madrid mai rike da Champions League na bara mai 14 jimilla, ita ce ta yi waje da Liverpool da Chelsea a kakar nan.