Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sterling bai aikata laifi ba - FA
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila (FA) ba za ta sake ɗaukar wani mataki kan Raheem Sterling ba bayan da ta yi nazarin bidiyon murnar cin ƙwallo ta farko da Chelsea ta yi a karawar da suka yi da Tottenham ranar Litinin.
An yi zargin cewa Sterling ya jefa wani abu a cikin 'yan kallo.
Ɗan wasan yana da damar karawa da tsohon kulob dinsa Manchester City ranar Lahadi a Stamford Bridge.
Blues ta samu nasara a wasan da suka buga da abokan hamayyarsu na Landan da ci 4-1 a wasan da aka bai wa Spurs jan kati biyu.
Ɗan wasan mai shekaru 28, wanda ya buga wa Ingila wasanni 82 kuma ya zura ƙwallaye 20.
Gareth Southgate bai shigar da ɗan wasan cikin tawagarsa ta ƙasa da ƙasa ba a karo na biyar a jere ranar Alhamis.
Ya zura ƙwallaye huɗu a raga kuma ya taimaka a ka ci biyu kawo yanzu a kakar wasa ta bana.