Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Super Eagles ta kai zagaye na biyu bayan cin Guinea-Bissau
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka, bayan cin Guinea-Bisau 1-0 ranar Litinin.
Wasa na uku-uku a cikin rukunin farko da aka buga kenan, inda a lokacin Equatorial Guinea ta caskara Ivory Coast 4-0.
Najeriya ta zura kwallo ne a minti na 36, bayan da Guinea ta ci gida ta hannun Opa Sangante.
Super Eagles ta ci kwallo biyu ana sokewa, ita ma Guinea-Bissau ta zura kwallo a ragar Nageriya, amma ba a karɓa ba.
Da wannan sakamakon Super Eagles ta kare a mataki na biyu a rukunin farko da maki bakwai, yayin da Equatorial Guinea ce ta yi ta ɗaya da maki bakwai iri ɗaya da na Najeriya.
Ivory Coast ta sha kashi a hannun Equatorial Guinea da ci 4-0 a ɗaya karawar rukunin farko.
Equatorial Guinea ta fara cin kwallo ta hannun Emilio Nsue, saura minti uku su je hutun rabin lokaci.
Mai masaukin baki Ivory Coast ta ci kwallo ta hannun Ibrahim Sangare, amma daga baya aka soke.
Daga baya Equatorial Guinea ta ƙara na biyu ta hannun Pablo Ganet da kuma Emilio Nsue da ya zura na uku a raga.
Saura minti biyu a tashi wasan Equatorial Guinea ta ƙara na huɗu ta hannun Jannick Buyla Sam.
Kai tsaye Equatorial Guinea ce ta ja ragamar rukunin farko da maki bakwai sai Najeriya ta biyu ita ma mai maki bakwai.
Tun a baya Equatorial Guinea ta ƙasa haura wasannin rukuni a gasar cin kofin Afirka biyu, amma ta ja ragamar rukunin farko a Ivory Coast.