Afcon 2023: Salah ba zai buga wa Masar wasa biyu ba

An wallafa

Mohamed Salah ba zai buga wa Masar karawar da za ta yi da Cape Verde ba ranar Litinin a gasar cin kofin nahiyar Afirka, sakamakon raunin da ya ji.

Haka kuma dan kwallon Liverpool ba zai yi wa Masar wasa daya a zagaye na biyu ba, koda Masar za ta kai zagayen kungiyoyin 16.

Salah ya ji rauni a wasan da Masar da Ghana suka tashi 2-2 ranar Alhamis a karawar cikin rukuni na biyu.

Kenan Salah zai kara buga wa Masar wasa ne idan tawagar ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe da za a yi ranar biyu da uku ga watan Fabrairu.

Tun a ranar Juma'a kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce Salah na tare da gajiya, wanda wasa 10 ne bai buga ba a lik a kaka shida a Liverpool.

Rashin Salah a tawagar Masar zai sa tawagar ta fuskanci kalubale a Afcon, bayan da ta fara wasannin da ake yi a Ivory Coast da kasa taka rawar da ta dace.

Salah ne ya ci Mozambique ranar Lahadi da suka tashi 2-2 a wasan farko a gasar kofin Afrka, sannan ta tashi 2-2 da Ghana.

Masar mai maki biyu a rukuni na biyu na bukatar cin Cape Verde mai maki shida, idan har tana son buga zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta Afirka.

Rabon da Masar ta dauki gasar kofin Afirka tun 2010, ita ce kan gaba a yawan lashe kofin mai bakwai jimilla.