Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mahamat Deby ya lashe zaɓen shugaban Chadi
Shugaban gwamnatin Chadi ta soji Mahamat Deby ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a makon da ya gabata.
Sakamakon farko-farko da hukumar zaɓe ta fitar ya nuna cewa Deby ya cinye kashi 61 na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da babban abokin hamayya kuma Firaminista Succes Masra ya zo na biyu da kashi 18.5.
Sakamakon na nufin an kawo ƙarshen gwamnatin riƙon-ƙwarya da Mahamat Deby ya shafe shekara uku yana jagoranta tun bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby.
Tun kafin zaɓen Mista Masra ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara, yana mai zargin cewa wasu na shirin jirkita sakamakonsa.
Kafin fara kaɗa ƙuri'a, 'yan adawa sun zargi cewa zaɓen wata hanya ce kawai ta halasta zaman Janar Mahamat Deby a kan mulki.
Ana sa ran majalisar tsarin mulki za ta sanar da sakamakon a hukumance bayan 'yan kwanaki.