Barca ta barar da damar bai wa Real tazarar maki 10 a La Liga

An wallafa

Barcelona ta yi nasara a gidan Almeria da ci 10 a wasan mako na 23 a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi.

To sai dai Almeria ta kawo karshen wasa 13 da Barcelona ta yi a jere a La Liga ba tare da an doke ta ba a bana.

Ranar 5 ga watan Nuwambar 2022, Barcelona ta ci Almeria 2-0 a Camp Nou a wasan farko da suka kara a La Liga.

Ousmane Dembele ya fara cin kwallo a ranar a minti na uku da komawa zagaye na biyu, sannan Frenkie De Jong ya zura na biyu a raga a minti na 62.

Yanzu saura maki bakawi tsakanin Barcelona mai matakin farko da maki 59 da Real Madrid ta biyu mai maki 52.

Ranar Asabar Real da Atletico Madrid suka tashi 1-1 a wasan hamayya a Santiago Bernabeu karawar mako na 23 a La Liga.

Kafin wasan Almeria tana mataki na 19 a kasan teburi da maki 22, doke Barcelona da ta yi ta koma ta 15 da maki 25, bayan wasa 23 a La Liga.

Robert Lewandowski ne kan gaba a cin kwallaye a La Liga a bana, mai 15 a raga.

Tuni Xavi Hernandez ya bayyana 'yan wasan da ya je da su Almeria:

Ciki sun hada da Ter Stegen, R. Araujo, Sergio, Gavi, Lewandowski, Ferran, Iñaki Peña, Christensen da kuma Marcos A.

Sauran sun hada da Jordi Alba, Kessie, S. Roberto, F. De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Balde, Pablo Torre da kuma Arnau Tenas.

Sakamakon wasannin mako na 23 da aka buga ranar Lahadi:

  • Athletic Bilbao 2 - 3 Girona
  • Celta Vigo 3 - 0 Real Valladolid
  • Almeria 1 - 0 Barcelona
  • Sevilla 0 - 1 Osasuna