Real Madrid za ta fafata da Arsenal, Man United na son ta raini Rigg don ya zama gagarabadau

.

Asalin hoton, Chriss Rigg

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool na sha'awar Aurelien Tchouameni - da kuma Bryan Mbeumo da Antoine Semenyo , yayin da West Ham ke son Igor Jesus da sauran su.

Liverpool na son inganta 'yan wasanta a watan Janairu kuma tana sha'awar sayen dan wasan tsakiyar Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 24, daga Real Madrid. (Teamtalk)

Dan wasan gaban Brentford na Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, da dan wasan gaban Bournemouth na Ghana, Antoine Semenyo, mai shekara 24, na cikin 'yan wasan da Liverpool ke zawarcinsu, yayin da dan wasan Masar Mohamed Salah, mai shekara 32, ke a shekarar karshe ta kwantiraginsa a Anfield. (Sky Sports)

West Ham na son sayen dan wasan gaban Botafogo na Brazil Igor Jesus, mai shekara 23, a kan fan miliyan 30. (Sun)

Manchester United na son siyan matashin dan wasa don ya zama fitaccen dan wasa a kungiyar, kuma ta yi imanin dan wasan da zai dace shi ne dan wasan tsakiyar Ingila Chris Rigg mai shekaru 17, wanda Sunderland ta masa kudi kan fan miliyan 20 zuwa 30. (Football Insider)

Yanzu Galatasaray na fatan daukar dan wasan Chelsea Victor Osimhen na dindindin, bayan da tuni ta karbe shi a matsayin aro na tsawon kakar wasa daga Napoli, inda kulob din na Turkiyya ya amince da biyan Yuro miliyan 50 (£42m) kan dan wasan Najeriyar mai shekara 25. (Sozcu Rnglish)

West Ham ta bi sahun kungiyoyi da dama da ke bibiyar dan wasan Atalanta na Najeriya Ademola Lookman, mai shekara 27. (Teamtalk)

Chelsea na zawarcin dan wasan gaban Borussia Dortmund dan kasar Jamus Karim Adeyemi, mai shekara 22, wanda Liverpool ke zawarcinsa a bazara. (Football Insider)

Real Madrid na iya yin hamayya da Arsenal da Chelsea kan sayen dan wasan baya na Brazil Vitor Reis mai shekaru 18 daga Palmeiras. (Athletic)

Dan wasan Manchester City Stefan Ortega yana kan radar Bayer Leverkusen amma har yanzu ba su kai ga cimma matsaya ba kan golan Jamus mai shekara 31. (Sky Sport Germany)