Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Hukuncin ƙin taimakon 'yansanda da ƙarin farashin man Dangote
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
A ranar Litinin da ta wuce ne rundunar ƴansandan Najeriya ta ankarar da al'ummar ƙasar cewa duk mutumin da ya ƙi taimakon jami'anta a lokacin da suke neman ɗauki, na iya fuskantar hukuncin ɗauri ko kuma tara.
Wannan na kunshe ne a wani bayani da rundunar ta wallafa a shafinta na X, a ranar inda ta ce, sashe na 99 na dokar ƴansanda ta ƙasar ta shekarar 2000 ya tanadi hakan.
"Duk wanda aka kira domin ya taimaka wa jami'in ɗansanda wanda - a sa'ilin gudanar da aikinsa ke fuskantar cin zarafi ko hantara ko turjiya - sai mutum ya ƙi, ko kuma ya yi watsi da buƙatar taimakawa, to wannan mutum ya aikata laifi, wanda zai iya janyo a yanke masa tarar naira 100,000 ko ɗaurin wata uku, ko kuma duka biyun idan aka same shi da laifi," kamar yadda bayanin ya nuna.
'Gobara ta laƙume kadarorin sama da naira biliyan 67 a 2024 a Najeriya'
Haka kuma a ranar Litinin din ne dai hukumar kashe gobara ta Najeriya ta ce gobara ta laƙume kadarorin aƙalla naira biliyan 67.1 a shekarar 2024 da ta wuce.
A wata sanarwa da tashar Channels ta ruwaito daga shugaban hukumar, Abdulganiyu Jaji a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya ce bayan asarar kadarorin, gobara ta kashe aƙalla mutum 100 a shekarar.
Sai dai ya ce hukumar ta taimaka wajen tseratar da kadarori na sama da naira tiriliyan 1.94, sannan sun taimaka wajen tseratar da sama da mutum 30,890.
Babban layin lantarkin Najeriya zai ci gaba da lalacewa - ministan lantarki
A ranar Talata da ta gabata ne ministan wutar lantarki na Najeriya ya ce, babban layin wutar lantarki na ƙasar zai ci gaba da fuskantar matsaloli sakamakon gazawar gwamnati wajen gyara wani muhimmin layin lantarki a arewacin Najeriya saboda rashin tsaro da ake fama da shi.
Adebayo Adelabu ya bayyana haka ne a yayin da yake magana a zaman kare kasafin kuɗin 2025 a gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa kan wutar lantarki.
Adelabu ya bayyana tasirin layin Shiroro-Kaduna-Mando da ya lalace, wanda ba ya aiki tun bayan lalata shi da aka yi a watan Oktoban 2024. Wannan gazawar ta sanya matsin lamba sosai a kan babban layin, wanda ke haifar da faɗuwarsa akai-akai.
CBN ya ci tarar bankuna saboda rashin saka kuɗi a ATM
A ranar Talatar da ta wuce ne Babban Bankin Najeriya CB ya fitar da wani bayani da ke nuna cewa ya ci tarar wasu bankunan kasuwanci na Najeriya saboda samun kuɗi a na'urorin cire kuɗi na ATM ɗinsu a lokacin bukuwan ƙarshen shekara.
Babban bankin ya ci tarar naira miliyan 150 ne kan kowane banki da ya samu da laifin, kuma bankunan sun haɗa da Fidelity da First Bank Plc da Keystone da Union da Globus da Providus da Zenith Bank da UBA da Sterling tarar naira miliyan 150.
A wata sanarwa da aka miƙa wa bankunan, an ce za a zare kuɗaɗen ne kai tsaye daga asusun ajiyarsu da ke babban bankin," kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Manufofin gwamnatin Najeriya sun tsunduma al'umma cikin talauci a 2024 - HRW
A wani rahoto da ta fitar ranar Laraba, da ta gabata, kungiyar kare hakkin bil'Adama ta Human Rights Watch ta ce sauye-sauyen tattalin arziki a Najeriya sun jawo mummunan talaucin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 30.
kuma babu wani tsari na hakika da gwamnati ta dauka domin magance matsalar, sai ma ta yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen hana zanga-zangar tsadar rayuwa.
A rahoton kungiyar na wannan sabuwar shekara ta kuma taɓo irin ta'asar da aka tafka na cin zarafin bil'Adama a kasashen Guinea, da Mali da Nijar da kuma Burkina Faso wadanda sun kara nuna irin gwamnatocin da ke shugabanci a yankunan.
Tinubu ya yaba wa gwamnonin Najeriya bisa amincewa da ƙudurin haraji
A ranar Juma'a ne Shugaba Tinubu ya yaba wa ƙungiyar gwamnonin Najeriya saboda amincewar da suka yi da ƙudurin yin gyara ga dokar haraji, wanda a yanzu ke gaban majalisar dokokin tarayya, domin neman amincewa.
Cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan yaɗa labarai da tsare tsare, Bayo Onanuga ya fitar, a ranar, Shugaba Tinubu ya jinjina wa gwamnonin kan sadaukarwarsu, da ya ce za ta samar da haɗin kai tsakanin shugabanni a ƙasar, ba tare da la'akari da ɓangaranci ko ƙabilanci ko kuma na siyasa ba.
Tinubu ya bayyana cewa babbar manufar sabon ƙudurin dokar harajin ita ce "taimaka wa talaka, da bunƙasa ƙasa a fannin tattalin arziƙi, da kuma janyo hankalin masu zuba jari na cikin gida da kuma waje.
Matatar Dangote ta ƙara farashin man fetur zuwa naira 955
Harwayau a ranar Juma'a ne da ta wuce matatar man fetur ta Dangote ta sanar da ƙara farashin man fetur zuwa naira 955.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma'a kan ƙara farashin man, inda matatar ta ce za ta riƙa sayar da kowace lita a kan farashin naira 955 ga kwastomomin da za su saya tsakanin lita miliyan biyu zuwa lita miliyan 4.99.
Sai dai sanarwa ta ce masu sayan fetur ɗin da yawa daga lita miliyan zuwa sama, za su riƙa saya ne a kan naira 950, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, a ranar.