Karo na uku a jere Brighton ta doke Man United a Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta yi rashin nasara 3-1 a hannun Brighton a Premier League da suka kara ranar Lahadi a Old Trafford.
Minti biyar da fara tamaula, Brighton ta ci ƙwallo ta hannun Yankuba Minteh daga baya United ta farke ta hannun Bruno Fernandes a bugun fenariti.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Brighton ta kara na biyu ta hannun Kaoru Mitoma, sannan Georginio Rutter ya kara na uku.
Karo na uku a jere da Brighton ke cin United a Old Trafford a Premier League.
Wasa uku da Brighton ta doke United a Premier a Old Trafford:
Lahadi 19 ga watan Janairun 2025
- Man United 1 - 3 Brighton
Asabar 16 ga watan Satumbar 2023
- Man United 1 - 3 Brighton
Lahadi 7 ga watan Agustan 2022
- Man United 1 - 2 Brighton
Haka kuma Brighton ta yi nasara a kan United a Premier League gida da waje a bana, wadda ta ci 2-1 ranar 24 ga watan Agustan 2024.
Da wannan sakamakon Brighton tana ta taran teburi da maki 34, ita kuwa United tana ta 13 da maki 26, bayan karawar mako na 22.
Ranar Alhamis United za ta buga Europa League a gida da Rangers ranar 21 ga watan Janairu daga nan ta je Fulham a Premier League ranar Lahadi 26 ga Janairu.










