Liverpool za ta yi bikin lashe Premier a cikin watan Mayu

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Liverpool, wadda ta lashe Premier League na 2024/25, za ta yi bikin ɗaukar kofin, kamar yadda mahukuntan suka sanar.

Liverpool ta doke Tottenham 5-1 a Anfield ranar Lahadi, hakan ya sa ta ɗauki Premier League na bana, kuma na 20 jimilla.

Za ta yi amfani da buɗaɗɗiyar motar bas ɗauke da ƴan wasa a samanta da za ta bi ta titin Allerton Maze ranar Litinin 26 ga watan Mayu.

Motar za ta yi tafiyar kilomita 15, tun daga Allerton Maze za ta bi ta Queens Drive zuwa The Strand daga nan ta karkare a Blundell.

Ana sa ran dubban magoya bayan Liverpool, za su tsaya a bakin titi, domin taya ƙungiyar da Arne Slot ya ja ragama murnar da ta lashe kofin kakar nan.

Bikin da mahukuntan birnin Liverpool za su tsara, ana sa ran zai ɗauki awa uku zuwa biyar daga nan kowa ya san inda dare ya yi masa.

Ana sa ran dubban makaɗa da mawaka za su gwangwaje a dandalin Sefton tun daga ranar Juma'a 23 zuwa Lahadi 25 ga watan Mayu.

Liverpool za ta buga wasan karshe a kakar bana ranar 25 ga watan Matu, wadda za ta karɓi bakuncin Crystal Palace a Anfield a Premier League.

Saura wasa hudu a kammala gasar Premier ta bana, Liverpool ta ci wasa 25 daga 34 da ta yi da canjaras bakwai aka doke ta wasa biyu kacal.

Arsenal ce ta biyun teburi da tazarar maki 15 tsakani da Liverpool, wadda ta lashe kofin bana, kuma yawan iri ɗaya da Manchester United ta ɗauka 20 jimilla.