Inter Miami na zawarcin De Bruyne, tauraruwar Diaz na haskawa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Inter Miami na da sha'awar ɗaukan Kevin de Bruynme idan ɗanwasan tsakiyar na Belgium mai shekara 33 ya bar Manchester City a ƙarshen kaka duk da cewa ba a tunanin tattaunawa ta yi nisa a wannan gaɓa. (Florian Plettenberg)

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Nassar ta Saudiyya na son ɗaukan ɗanwasan Liverpool Luis Diaz mai shekara 28 a madadin ɗanwasan Real Madrid Vinicius Jr. (Talksport)

Everton ta zama ƙungiya ta baya-bayan nan da ta shiga fagen tseren zawarcin ɗanwasan Ingila a matakin ƴan ƙasa da shekara 21 Liam Delap mai shekara 22 daga Ipswich Town. (Sun)

Newcastle na zwarcin ɗanwasan tsakiya na Girka Konstantinos Karetsas mai shekara 17 amma tana fuskantar gogayya daga Bayern Munich da Napoli da wasu ƙungiyoyin Premier. (Sun)

Newcastle ta tura wakilai su sa ido kan ɗanwasan Ivory Coast Yahia Fofana mai shekara 24 a ƙungiyar Angers yayin da take shirin ƙarfafa zaɓinta na gola. (Football Insider)

Arsenal na nan kan bakanta na zawarcin ɗanwasan Ajax mai shekara 19 Jorrel Hato a bazara duk da cewa duk wata yarjejeniya kan ɗanwasan na iya dogaro ne kan makomar Jakub Kiwior. (Mirror)

Arsenal ba ta da shirin sayen ɗanwasan Chelsea da Ingila Raheem Sterling mai shekara 30 a matsayin aro a matakin dindindin. (Football Insider)

Chelsea da Bournemouth na shirin biyan euro miliyan 35 domin sayen ɗanwasa Johnny Cardoso mai shekara 23 daga Real Betis ta Sifaniya. (Fichajes - in Spanish)