Guardiola ya ɗauki alhakin rashin kokarin Man City

Pep Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola ya ce ya ɗauki alhakin rashin kokarin da ƙungiyar ke fuskanta a wasanninta.

City, mai rike da Premier League, kuma huɗu a jere, mai guda shida a kaka bakwai baya tana da tazarar maki 14 tsakaninta da Liverpool mai jan ragama.

Ranar Lahadi City ta doke Leicester City 2-0 a Premier League, karo na biyu da ta ci wasa daga dukkan karawa 14 da canjaras uku aka doke ta tara daga ciki.

Rashin nasara mai yawa da Guradiola ya fuskanta tun bayan da ya horar da Barcelona da Bayern Munich da kuma City.

''Da zarar ana cin ƙungiya a wasa da yawa ya zama wajibi koci ya ɗauki alhaki. Akwai wani abun da ya kamata mu yi tare da ƙwarin gwiwa, abinda na kasa kenan.

''Wannan alhaki nane bana ƴan wasa ba. Sun ɗan yi kasa a sa ƙwazo, kuma hakan kan faru ba wani abu bane, kuma mun yi haka a bara.''

City kan fara kaka da rashin ƙwazo a baya - sai ta yi gaba har da bayar da tazarar a kaka huɗu baya har ta kai ga lashe Premier, amma ba ta taɓa samun kanta a irin wannan halin ba.

Ƴan wasan City da yawa na fama da jinya a kakar nan - har da wanda ya lashe ƙyautar Ballon d'Or, Rodri, wanda Guardiola ke bayar da misalin hakan.

''Mun daɗe ba a doke mu ba a wasanni a Turai har zuwa karshen Oktoba, kuma muna kan teburi, daga baya abubuwa suka lalace mana, sakamakon ƴan wasan mu dake jinya da sauransu.''

City za ta ƙarbi bakuncin West Ham United a wasan mako na 20 a Premier League ranar Lahadi.