Cibiyar da dakarun gwamnatin Assad ke miƙa makamansu

    • Marubuci, Yogita Limaye
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Correspondent
    • Aiko rahoto daga, Damascus
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ranar shida ga Nuwamba da dare, Mohammed el-Nadaf, wani sojan Syria yana wurin yai a Homs

Yayin da ƴantawaye ƙarƙashin jagorancin Hayat Tahrir al-Sham HTS suka doshi birnin, kwanaki bayan sun ƙwace ikon Aleppo da Hama, Mohammed ya yanke shawarar ba zai shiga yaƙin ba.

"Babu wani umarni ba labari. Na cire kakin soja, na bar makamai sannan na kama hanyar shiga ƙauyenmu na Tartous," in ji shi.

A lokacin ne, Mohammed Ramadan shi ma yana inda da aka ajiye shi wurin yaƙi a wajen Damascus.

"Babu kowa da zai ba mu umarni. Kwamandojinmu da dama sun gudu, daga nan na fara tunanin mai zai sa na mutu na yi wa wani yaƙi wanda ko albashin kirki ba ya ba ni da zai wadatar da iyali na."

"A matsayinmu na sojoji a rana ƙwai ɗaya da dankali muke samu."

Da wayewar gari shi ma ya fice ya nufi hanyar gida.

Kalaman sojojin ya bayar da haske yadda aka kawo ƙarshen gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Sojoji da dama sun shaida muna cewa ana biyansu albashi ƙasa da dala 35 a wata, dole sai sun haɗa da wani aikin domin biyan buƙatunsu.

Mohammed Ramadan yana riƙe da bindiga kirar Kalashnikov da aka ba shi lokacin da muka same shi haka ma sauran sojojin da dama a Damascus makwanni biyu bayan faɗuwar gwamnatin Assad, a cibiyar sasanci ƙarƙashin kulawar HTS.

A cibiyar, tsoffin sojoji da ƴansanda da jami'an leƙen asiri. da dukkanin mayaƙan da ke goyon bayan gwamnatin Assad, za su iya rijistar samun katin shaida na farar hula tare da miƙa makamansu.

HTS ta sanar da yin afuwa ga kowa waɗanda suka yi aiki da tsohuwar gwamnati..

Waleed Abdrabuh, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke kula da cibiyar a Damascus, ya ce "manufar ita ce karɓar makaman da hamɓararriyar gwamnati ta bayar ga sabuwar gwamnatin Syria. Sannan sojoji su samu shaidar zama farar hula domin shiga al'umma."

A zamanin Assad, aikin soja dole ne ga maza, inda ake musanya masu katin shaida zuwa na soja.

Duk wanda ba shi da katin shaida samun aiki zai yi masa wahala da kuma samun damar yin walwala a ƙasar, dalilin da ya sa dubban mutane suka yi dandazo a cibiyoyin rijistar.

A cibiyar da ke Damascus, tsohon ofishin jam'iyyar Assad, dubban mutane ne suka cika makil a kofar shiga suna jiran samun damar shiga.

Suna son su nesanta kansu da tsohuwar gwamnati.

"Ban sa kaina ba cikin munanan ayyukansu ba. Na yi koƙarin kaucewa shiga duk wani aiki na kisan kiyashi da kuma laifuka cin zarafi ga ƴan Syria," a cewar Mohammed al-Nadaf

"Na sha ƙoƙarin barin aikin soja har sau biyu amma na san da wahala mutum ya iya tserewa. Rundunar sojin tana da dukkanin takarduna."

Somar al-Hamwi, wanda ya shafe shekara 24 a soji ya ce: "Galibin mutane ba za su san komi ba, kuma ni ban san abin da ya faru ba a Saydnaya ko ɗaya daga cikin gidajen yari."

BBC ba za ta iya tabbatar da wannan iƙirarin ba.

Adawa da gwamnatin da kuma matakin Assad na tserewa zuwa Rasha a ranar 7 ga Disamba yayin da ƴantawaye suka nufi Damascus ya ƙara fusata mutane.

"Shi Bashar al-Assad ya kwashi kuɗi da dama ya tsere. Ya bar dukkanin waɗannan mutane, ya bar mu sojoji mu san yadda za mu yi," in ji Somar.

Akwai fuskoki da dama da ke cike da damuwa a cikin dandazon mutanen da suka taru a cibiyar, amma wurin ba hayaniya duk da yakin shekara 13 da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da rabin miliyan.

Sai da a wasu sassan Syria akwai rahotanni na zargin hare-haren ramuwa da kisa da satar mutane da ke ƙaruwa. Babu wasu sahihan bayanai da za su tabbatar da hare-haren sun faru amma an bayar da rahoton da dama a kafofin sada zumunta na intanet.

Nadine Abdullah, matar Mounzer ta shaida muna cewa mijinta ya fuskanci barazana saboda shi Alawite ne - tsiraru ƴan ƙabilar Assad.

Nazir ɗan'uwan Mounzer ya ce: " wannan laifi ne kan waɗanda ba su ba su gani ba. Ba za a lamunce ba. Waɗanda aka kashe ba su da alaƙa da siyasa ko gwamnatin Assad.

Mounzer yana da ƴaƴa huɗu, ma'aikaci ne da ke kula da mahaifinsa da kuma ɗan'uwansa

An kashe shi kuma danginsa sun ce suna magana ne don hana sake aukuwar irin kisan a nan gaba.

"Kowa ya ce HTS ba ita ce ta yi kisan ba. Amma kasancewarta kan madafan iko a yanzu, haƙƙinsu ne su gano waɗanda suka aikata. Dole su kare mu duka," in ji Nadine.

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta HTS ta yi allawadai da kisan alkalai inda ta ce za ta gano waɗanda suka aikata kisan. Kuma ta musanta hannu a hare-haren.

An yi zanga-zanga a Masyaf bayan kisan alkalai, kuma ƴan kabilar alawite sun shaida wa BBC cewa sun fargaba kan rayuwarsu.

Yayin da HTS ta bayyana yin afuwa ga dakarun Assad, ta kuma cewa waɗanda suka aikata kisa da azbatarwa za su fuskanci hukunci.