Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Solskjaer zai koma horar da ƙungiyar Besiktas
Tsohon kocin ƙungiyar Manchester, Ole Gunnar Solskjaer zai koma ƙungiyar Besiktas domin karɓar ragamar horar da ƴanwasanta.
Tsohon kocin mai shekara 51 zai dawo aikin horar da ƴanwasa ne tun bayan da Manchester United ta sallame shi a shekarar 2021.
Besiktas, wadda ke mataki na shida a teburin gasar Super Lig ta Turkiyya, ta sallami tsohon kocinta Giovanni van Bronckhorst ne a watan Nuwamban bara.
"Na yi farin cikin kasancewa a wannan ƙungiya," in ji Solskjaer a zantawarsa da manema labarai a filin jirgin saman Ataturk da ke Turkiyya.
"Mun yi zama na farko inda muka fara tattaunawa, kuma har na ƙosa in fara aiki. Abin farin ciki ne in zama kocin wannan ƙungiya."
Solskjaer ne ya maye gurbin Jose Mourinho a matsayin kocin Man United na riƙon ƙwarya a watan Disamban 2018, sannan a watan Maris na 2019 ya sa hannu a kwantiragin horar da ƙungiyar na shekara uku.
Kafin Manchester United, ya horar da ƙungiyar Molde da Cardiff City.
Ya buga wa Manchester United a tsakanin 1996 zuwa 2007, inda ya zura ƙwallo 126. Yana cikin ƴanwasan ƙungiyar da suka lashe gasar Champions League ta 1999.