Inter Miami ta kusa cimma yarjejeniya da Messi, Man Utd ta yi wa Hojlund farashi

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta saurari tayin fam miliyan 52 kan ɗanwasan Denmark Rasmus Hojlund yayin da Juventus ke zawarcin ɗanwasan mai shekara 22. (Tuttomercatoweb - in Italian)
Sai Manchester City ta biya fam miliyan 100 idan tana son ɗaukan ɗanwasan Ingila da Nottingham Morgan Gibbs-White mai shekara 25 a bazara. (Talksport)
Real Madrid za ta yi amfani da lokacinta a fafatukar neman ɗanwasan Arsenal William Saliba mai shekara 24 da nufin rattaba hannu kan yarjejeniyar rage farashinsa a 2026 idan kwantiraginsa ya kare a 2027. (Athletic - subscription required)
Kocin Manchester United Ruben Amorim zai tattauna da ɗanwasan gaba na Ingila Marcus Rashford a wannan bazarar idan ɗan shekara 27 ɗin bai ƙulla yarjejeniyar dindindin da Aston Villa ba. (Daily Star)
Manchester City na ci gaba da tattaunawa kan sabon kwantiragin ɗanwasan tsakiya na Ingila na ƴan ƙasa da shekara 20 Nico O'Reilly bayan Chelsea ta nuna sha'awarta kan ɗanwasan mai shekara 20 a watan Janairu. (Fabrizio Romano).
Inter Miami ta kusa cimma yarjejeniya da shararen ɗanwasan Argentina Lionel Messi mai shekara 37 kan tsawaita kwantiraginsa a kulob din MLS. (Athletic - subscription required)
Ɗanwasan tsakiya na Real Betis Sergi Altimira, 23, zai ƙulla sabon kwantiragi har zuwa 2029 duk da sha'awar da Manchester City ta nuna kan ɗanwasan. (Fabrizio Romano)
Manchester United da Newcastle da Arsenal da Aston Villa da Nottingham Forest and Tottenham na zawarcin ɗanwasan Wolves da Brazil mai shekara 25 Matheus Cunha. (Daily Mail)










