An ci Real Madrid karo na biyu a gida bayan da Milan ta doke ta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

AC Milan ta je ta doke RReal Madrid 3-1 a Champions League da suka fafata ranar Talata a Champions League.

Milan ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Thiaw a minti na 12 da take leda daga baya Real Madrid ta farke a minti na 23 ta hannun Vinicius Junior.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Milan ta kara na uku ta hannun Alvaro Morata, sannan Reijnders ya zura na huɗu saura minti bakwai a tashi daga karawar.

Wannan shi ne wasa na 16 da suka fafata a tsakaninsu, inda Real ta yi nasara shida, Milan ta ci wasa bakwai da canjaras uku.

Karo na biyu da Milan ta doke Real a Santiago Bernabeu a gasar zakarun Turai, bayan 3-2 da ta ci ranar 21 ga watan Oktoban 2009.

Ƙungiyoyin biyu sun lashe Champions League 22 a tsakaninsu, inda Real Madrid mai rike da kofin take da 15, ita kuwa Milan ta ɗauki bakwai.

Sai dai rabon Milan da Champions League tun kakar 2006/07, wadda ta doke Liverpool 2-1 a wasan karshe a lokacin.

Wannan shi ne karo na biyu a jere da Real ta yi rashin nasara a Bernabeu, bayan da Barcelona ta zura mata 4-0 a El Clasico ranar 26 ga watan Oktoba.

Ƴan wasan Real Madrid da suka fuskanci Milan:

Masu tsaron raga: Lunin, Fran González da kuma Mestre.

Masu tsare baya: Militão, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger da kuma Mendy.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Ceballos.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Mbappé, Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.

Sakamakon wasannin da aka buga ranar Talata a Champions League:

PSV 4 - 0 Girona

Slovan Bratislava 1 - 4 Dinamo Zagreb

Bologna 0 - 1 Monaco

Borussia Dortmund 1 - 0 Sturm Graz

Celtic 3 - 1 RB Leipzig

Lille 1 - 1 Juventus

Liverpool 4 - 0 Bayer Leverkusen

Real Madrid 1 - 3 AC Milan

Sporting CP 4 - 1 Manchester City