Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Fashewar tankar mai a Jigawa da bulaguron Tinubu da Shettima
Wannan maƙale ce da ke kawo muku bitar muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
Fiye da mutum 170 sun mutu a fashewar tankar mai a Jigawa
Babban labarin da ya fi jan hankali a wannan makon shi ne labarin fashewar wata tankar dakon man fetur a yankin ƙaramar hukumar Taura da ke jigawa.
Lamarin ya faru ne da ranar Talata da daddare bayan da tankar ta yi hatsari a daidai garin Majiya.
Bayan faɗuwar motar mutane sun fita, cikin daren inda suka riƙa kwasar man da ya malala bayan faɗuwar motar.
A daidai lokacin ne kuma wuta ta kama, lamarin da ya sa motar ta fashe, abinm da kuma ya yi sanadnin mutawar mutane da dama tare da jikkata gommai.
Mutane da dama ne suƙa ƙone ta yadda ma ba za a iya gane su, lamarin da ya sa aka binne mutum 104 a kabarin bai ɗaya kusa da wurin da abin ya faru.
Tuni dai gwamnatin Jiagwa ta ƙaddamar da asusun tallafa wa waɗanda suka jikkata da iuyalan waɗanda suka rasu.
Bulaguron Shettima bayan tafiyar Tinubu hutu
Wani labari da ya sake jan hankali a Najeriya cikin wannan mako shi ne labarin tafiyar mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima taron ƙulla yarjejeniyoyi tsakanin ƙasashe zuwa ƙasar Sweden.
Tafiyar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban ƙasar Bola Tinubu ke hutun mako biyu da ya bayyana tafiya zuwa Birtaniya tun ranar 3 ga watan Oktoba, kodayake daga baya fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa ya zarce zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa.
Bulaguron jagororin ƙasar biyu zuwa ƙasashen waje a lokaci guda ta ja hankali, lamarin da ya ya wasu 'yan ƙasar da masu suka suka riƙa ce-ce-ku-ce kan wa ke jagorantar ƙasar a wannan lokaci.
Wannan al'amari ya sa fadar shugaban ƙasar ta mayar da martani, mata mai cewa babu wani giɓin shugabanci a ƙasar, kasancewar shugaban ƙasa da mataimakinsa ba sa ƙasar.
A cewar sanarwar wadda mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce rashin jagororin biyu a cikin ƙasare ba shi ke nuna samun giɓin shugabanci a ƙasar ba, saboda akwai sauran ƙusushin gwamnatin da ke gudanar da duk wasu ayyukan gwamnati.
Fadar shugaban Najeriya ta yi martani kan rahotannin tsige Akpabio
Makon ne kuma fadar shugaban Najeriya ta yi watsi da wasu rahotanni da ke yawo a ƙasar na shirin tsige shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Godswill Akpabio daga kan muƙaminsa.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban na Najeriya ta fitar, ta jaddada cewa, shugaba Bola Tinubu ya ƙuduri aniyar samar da kyakkyawar alaƙa a tsakanin sanatoci, saboda muhimmiyar rawar da majalisar ke takawa wajen ci gaban ƙasa.
A ranar Laraba ne bayanai suka rawaito yadda aka samu tarin motocin jami’an tsaro na farin kaya na DSS a harabar majalisar, bayan ɓullar rahotanni zargin cewar wasu daga cikin sanatocin majalisar ta goma na shirin tsige Akpabio daga shugabancin majalisar.
A cewar mai bai wa shugaban na Najeriya shawara kan harkokin Majalisar Dattawan ƙasar Sanata Bashir Garba Lado, babu ƙanshin gaskiya kan labarin, wanda wasu daga cikin kafafen yada labarai Najeriya suka yaɗa.
Ko za a kore ni daga APC ba zan daina faɗar gaskiya ba - Ndume
Ɗan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume ya ce zai ci gaba da faɗa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu gaskiya, ko da hakan zai janyo masa kora daga jam'iyyar.
Sanata Ali Ndume ya ce: "Kowa ya san abin da ke faruwa a ƙasar nan. Kowa yana ji a jikinsa. Kuma ba laifi ba ne in gaya ma shugaban ƙasa don a kawo gyara".
Sai dai ga dukkan alamu, ko Shugaba Tinubu bai ga laifin waɗannan kalamai ba, to ran jam'iyyarsa ta APC ya ɓaci, abin da ya sanya ta fitar da sanarwa tana yi wa Sanata Ndume gargaɗi.
APC ta nunar cewa Ali Ndume, babban ɗan jam'iyya ne kuma sanata sannan yana da ƙima sosai a idonta da kuma jama'a, don haka in ji ta, bai kamata duk lokacin da za a ambace shi, sai a ce ya yi wani abu da zai tozarta jam'iyya ba.
Tinubu ya buƙaci CAF ta ɗauki mataki kan Libya
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci a gaggauta bincike, tare da tabbatar da hukunci na adalci game da tirka-tirkar da ta faru da ƴanwasan Super Eagles a Libya.
Tinubu ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai shi shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.
A farkon makon da ya gabatan ne 'yan wasan Najeriya da suka je Libya domin wasan neman gurbin kofin Afirka suka maƙale a wani filin jirgin saman Libya, lamarin da ya sa daga ƙarshe 'yan wasan suka koma gida, ba tare da buga wasan ba.
Tinubu ta buƙaci kwamitin ladabtarwa na CAF, "ta yi bincike, sannan ta bayar da shawarwarin irin hukuncin da ya kamata a ɗauka a kan waɗanda suka saɓa ƙa'idoji da dokokin hukumar."
Shugaban ya kuma yaba da ƙoƙarin ma'aikatar harkokin ƙasashen waje da ma'aikatar wasanni bisa ƙoƙarin da suka yi wajen shawo kan lamarin.