Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fadar shugaban Najeriya ta yi martani kan rahotannin tsige Akpabio
Fadar shugaban Najeriya ta yi watsi da rahotannin da ke yawo a ƙasar na shirin tsige shugaban Majalisar Dattawan kasar Godswill Akpabio daga kan mukaminsa.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban na Najeriya ta fitar, ta jaddada cewa, shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar samar da kyakkyawar alaka a tsakanin sanatoci, saboda muhimmiyar rawar da majalisar ke takawa wajen ci gaban kasa.
A jiya Laraba ne bayanai suka rawaito yadda aka samu tarin motocin jamai’an tsaro na farin kaya na DSS a harabar majalisar, bayan ɓullar rahotanni zargin cewar wasu daga cikin sanatocin majalisar ta goma na shirin tsige Akpabio daga shugabancin majalisar.
A cewar mai ba wa shugaban na Najeriya shawara kan harkokin Majalisar Dattawan ƙasar Sanata Bashir Garba Lado, babu ƙanshin gaskiya kan labarin, wanda wasu daga cikin kafafen yada labarai Najeriya suka yada.
“Lokacin da lamarin ya faru ina ofishina da ke majalisar, kuma nan take na futo bakin majalisar don ganin ko me ke faruwa, na tabbatar babu wani abu kamar hakan, illa ko wani bako ne da bai saba shigowa Majalisar ba ya shigo, ya ga yadda tsaron majalisar ya ke, ya yi zaton haka, tunda a majalisa akwai jami’an tsaro na DSS, da ƴan sanda, da ke aikin bayar da tsaro a majalisar, wannan ba wani sabon abu bane'' in ji Sanata Bashir Garba Lado.
To sai dai wani abun jan hankali shi ne yadda ba Majalisar ba ce ko wasu ƴaƴanta suka musanta fauruwar wannan lamari, duba da cewa ita ma na zaman cin gashin kanta ne, sai fadar shugaban ƙasar ke ke musantawa.
Hakan ya sa wasu jefa ayar tambaya kan ko me yasa bangaren gwamnati ya yi uwa ya yi makarɓiya kan batun, tare da musanta faruwar yunkurin tsige shugaban majalisar dattawan?
Sai dai sanata Bashir Garba Ladon ya ce hasashe ne kawai mutane ke yi sannan kuma ya ce “ni da kai na na ji yan majalisar na ƙaryata wannan lamari, wanda kuma nan da an jima zaka ji sauran jaridu sun ɗauka” in ji shi.
Haka kuma ya ce “ina tabbatar maka cewar babu wani abu mai kama da haka, illa kurum ko yaushe ita gwamnati musamman shi shugaban kasa, da ya taba zama dan majalisar dattijai a baya, ya san mahimmancin zaman lafiya a zauren majalisar dattawa da ta wakilan" a cewar Sanata Bashir Garba Lado.
Mai bai wa shugaban na Najeriya shawara kan harkokin majalisar dattawan ya ce ko kadan babu wani zance na rufe batun daga banagren fadar shugaban kasar.
A cewarsa ''Ba wai muna wadannan kalamai ne don lullubawa shugaban Majalisar rigar kariya ba, ko kadan babu wannan batu, illa magana ce da ke da alaƙa da musanta wannan yunƙuri na tsige shugaban majalisar dattawan Godswill Akpabio daga kan kujerarsa.