Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ƴan ci-ranin Afirka da ke Amurka ke rayuwa cikin fargaba kan korar baƙi
- Marubuci, Yusuf Akinpelu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Fargabar kai samame da tsarewa da fitar da su daga ƙasar, su ne manyan abubuwan da ƴanciranin Afirka da ke zaune a Amurka ke fuskanta, lamarin da ke tilasta wa wasunsu rayuwar ɓuya.
Ƴanciranin sun bayyana wa BBC cewa wasu ba sa fita daga muhallansu, wasu ba su zuwa aiki, wasu na taƙaita ziraga-zirga a wuraren a jama'a ke taruwa, yayin da wasu suka hana ƴaƴansu zuwa makaranta aboda fargaba kamu da tsarewa daga jami'an shige da fice na ICE
Ɗaya daga cikin ƴanciranin shi ne Kaduli, mutumin Kongo, wanda ya shiga Amurka shekara 11 da suka gabata.
An haifi Kaduli a Bukavu da ke wajen birnin Goma - da a baya-bayan nan 'yantawayen M23 suka ƙwace, a gabashin DR Kongo,.
Likita ne kafin ya fice daga ƙasar domin gujewa kamu bayan da ya soki shugaban ƙasar na wancan lokaci, Joseph Kabila, kan gyara kundin tsarin mulkin ƙasar don tsawaita wa'adin mulkinsa.
Kaduli ya shaida wa BBC cewa a yanzu ya rage zirga-zirgarsa a Amurka, ciki har da zuwa wuraren ci abinci da kantunan sayayya, saboda fargabar fitar da shi daga ƙasar.
"Samamen da aka fara a baya-bayan nan ya haifar mana fargaba saboda suna ɗaukar duk wani ɗancirani a matsayin mai laifi, wanda kuma a gaskiya ba hakan ba ne,'' in ji shi.
"Ina cikin fargaba saboda a yanzu haka Kongo na fuskantar yaƙi, tana cigaba da fuskantar mulkin zalunci. Mayar da mutum ƙasar tamkar aika shi lahira ne."
Kamar dai Kaduli, Abdul, daga Najeriya shi ma na fama da irin wannan fargaba.
Ya je Amurka tare da mahaifinsa shekara 30 da suka gabata, a lokacin yana da shekara 10.
"A yanzu ina ƙoƙarin taƙaita yawona, kuma na sani da izinin Allah ba abin da zai faru,'' a cewar mazaunin jihar Wisconsin ɗin.
Abdul ya ji kuma ya ga yadda jami'an ICE ke aiwatar da kamen a wasu biranen. Yana kuma fargabar fuskantar hakan.
"Yadda suke yi wa mutanen akwai takaici, kamar ba 'yan'adam ba, mu ma fa mutane ne, masu yanci," in ji shi.
Duka 'yanciranin da muka zanta da su a wannan rahoto, sun buƙaci mu bayyana su da sunayen iyayensu, saboda fargabar da suke ciki.
Gagarumar korar baƙi
Tun bayan komawarta fadar White House a watan Janairu, gwamnatin Trump ta ci gaba da matsala lamba kan dokokin korar baƙi, inda jami'an suka riƙa kai samame kan ƴancirani a manyan birane.
Gwamnati ta riƙa umartar sojoji su taimaka wa jami'an shige da fice domin yin kamen a wuraren da jama'a ke taruwa, kamar makarantu da coci-coci da asibitoci, lamarin da ya haifar da suka daga ƙungiyoyin kare ƴancirani.
Dubban mutane, masu laifi da marasa laifi ne aka tsare.
A makon da ya gabata ne jami'an ICE suka tsaurara kamen, inda suke tsare kusan mutum dubu a kowace rana.
Saɓanin gwmanatin Biden da ta riƙa fitar da baƙin haure a ƙalla 311 galibi masu laifi a kowace rana, a cewar hukumar ICE.
Pious Ali, kansilan gundumar Portland a jihar Maine, ya ce yayin da ba sabon abu ba ne korar baƙi, amma hanyar da ake bi a yanzu ta saɓa wa doka, musamman yadda ake kai samame makarantu da wuraren ibada tare da ''holen mutane'' kamar wasu masu laifi.
Ya ce ga ƴanciranin da cikin fargaba, yana da kyau su ''tara kudi da abinci sanna su tare a gida tare da iyalainsu''.
"Idan jami'an suka ƙwanƙwasa maka gida, kawai ka yi shiru, tunda doka ba ta ba su damar shiga gidan mutum ba, ba tare da umarnin kotu ba,'' in ji shi.
Kariyar wucin-gadi
Da dama daga cikin ƴanciranin Afirka na zama cikin ɗar-ɗar saboda halin rashin tabbas da suke ciki, idan wa'adin kariyar wucin gadi da ƙasashensu ke da shi ya cika.
Waɗannan ƴancirani daga ƙasashen da aka ƙebe - galibi masu masu da rikicin ƴanbidiga, ko wata bala'i - na da damar zama a Amurka su kuma nemin aikin yi.
Sylvie Bello, shugabar ƙungiyar 'Yan Kamaru mazauna Amurka (CAC), wata ƙungiya mai shalkwata a birnin Washington da ke rajin kare ƴanciranin yankin tsakiyar Afirka, ta ce halin da suke ciki ya faru ne sakamakon tsare-tsaren gwamnati Biden da ya shuɗe.
Ta ce ƙungiyar ta saka ran cewa Mista Biden zai tsawaita kariyar wucin-gadi ga ƙasashen Angola da DR Kongo a lokacin da ya ziyarci ƙasashen a watan Nuwamban bara, bulaguro ɗaya tilo da ya yi a nahiyar Afirka tun bayan hawansa mulki.
"Amma sai ya kasa yin hakan," in ji shi.
"Ƴan Afirka baƙaƙen fata na fuskantar barazanar rashin tsawaita wa'adin kariyar wucin-gadi a ƙarƙashin gwamnatin Trump,'' in ji shi.
Wa'adin kariyar wucin-gadi da ƴanciranin - Kamaru da Ethiopia da Sudan ta Kudu ke da shi za ta ƙare a ƙarshen wannan shekara, yayin da na ƴan Somaliya da Sudan zai ƙare a 2026.
Zaman ɗarɗar
A shekarun baya-bayan nan, ƴan Afirka sun ƙara mayar da hankali wajen cirani a Amurka bayan da suek bi ta ƙasashen Kudancin ƙasar da Mexico.
''Hakan baya rasa nasaba da irin wahalar da ake shiga ta hanyar tsallaka tekun Mediterranean,'' a cewar Nneka Achapu, wata ƙwararriya kan manufofin Afirka a Amurka.
Cikin wani rahoton shekara-shekara da jami'an ICE suka fitara a 2024ya nuna cewa kusan ƴan Afirka 1,818 aka fitar da su daga Amurka, inda ƙasashen Senegal da Mauritania da Najeriya ke kan gaba.
Daga cikin mutum miliyan 1.4 da aka fitar zuwa Nuwamban 2024, kashi uku ne kawai cikin adadin ƴan Afirka.
Somaliya ce kan gaba a Afirka, da mutum 4,090, daga nan sai Mauritania da mutum 3,822 sai Najeriya da 3,690 sai kuma Ghana mai mutum 3,228.
Sanin cewa akwai umarnin ƙarshe na koarar baƙi na ƙara zaman rashin tabbas tsakanin ƴanciranin Afirka.
"Dole mu ci gaba da rayuwa cikin halin rashin tabbas har na tsawon shekara huɗu, ko zuwa lokacin da zai ɗauka,'' in ji Abdul.
To sai dai ƙwararriyar kan tsare-tsaren Amurka kan Afirka, Nneka Achapu, ta ce wanna yanayi, wata dama ce da ƴan Afirka za su nuna juriya.
''Wannan dama ce ga gwamnatocin Afirka su fahimci tushen matsalolin da ke haddasa ficewar al'umominsu, su magance su tare da samar da ayyukan yi ga al'umominsu,'' in ji Ms Achapu.
"Haka ma idan Amurka ta ci gaba da korar baƙi, China da RAsha ka iya amfani da wannan damar wajen faɗaɗa tasirinsu a Afirka, inda za su buɗe wa 'yanciranin ƙofa zuwa ƙasashensu'', kamar yadda ta yi ƙarin haske.
Kaduli, tsohon likitan daga DR Congo, na da saƙo ga shugaba Trump.
"Domin sake inganta Amurka, ƙasar na buƙatar aiki da dokokin kare haƙƙin bil'adama tare da la'akari ƴancirani masu fikira da ƙwaƙwalwa da za su iya amfanar ƙasar wajen gina tattalin arzikinta,'' in ji shi.
"Ina kira ga shugaba ƙasa ya sanya jinƙai a gaba maimakon siyasa.'