Matsalolinmu ne a gabanmu - Amorim

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Mancheter United Ruben Amorim ya ce ƙungiyar ta mayar da hankali ne kan matsalolin gabanta maimakon magana kan abokiyar hamayyarta City da za su fafata a Etihad a ranar Lahadi.

Gwarzuwar Premier ta samu nasara ne a wasa ɗaya cikin 10 a duka gasannin da take yi, bakwai sun yi rashin nasara abin da ya dawo da su mataki na hudu da maki takwas tsakaninsu da Liverpool da ke saman teburi kuma tana da wasa guda da ya mata kwantai.

Amorim ya ci wasa uku cikin shida da ya jagoranci United a duka gasanni, ta kuma yi rashin nasara sau biyu a jere a Premier ta dawo matsayi na 13 a teburi.

Duk da cewa City ba ta ƙoƙari, ɗan ƙasar Portugal ɗin ya ce: "Ban taɓa tunani ba kan irin wannan tunanin. Za mu tunkari abokan wasa masu kyau, to ni na fi maar da hankali kan matsalolinmi, saboda muna da kalubale da dama a nan.

"Ni damuwata shi ne abin da za mu yi a ranar Lahadi mu samu nasara a wasan, kuma tuni na mayar da hankali kan tawagata."

An tambaye shi ko ya raina ƙarfin City - a matsayinsa na wanda ya cinyeta 4-1 lokacin da yake Sorting a CHampions Lig a watan Nuwamba - sai Amorim ya ce: "a'a, sam, ko da wasa.

"Manyan ƙungiyoyi za su iya mayar da martani a kowanne lokaci, kuma ina ganin sun fi mu dama idan aka yi la'akari da yadda suka fahimci Premier, yadda suke wasa da kwarin gwiwarsu. Ko da a irin wannan lokacin ne.

"Muna da abubuwa da dama a gabanmu. muna da dabarun da muke gwadawa na samun nasara a wasanni, amma dai hankalinmu na kan tawagarmu."