An buƙaci Arsenal da ta raba gari da ƙasar Rwanda

Asalin hoton, Getty Images
Magoya bayan Arsenal da dama da ke fafutukar ganin ƙungiyar ta gasar Premier ta yi watsi da batun sabunta yarjejeniyar ɗaukar nauyin da ke tsakaninta da ƙasar Rwanda, sun yi kira ga hukumar ta kulob ɗin da ta " ajiye batun ribar kuɗi a gefe".
Ƙungiyar Gunners for Peace ta ƙara da cewa ta gwammace a tallata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham, wanda ita ce babbar abokiyar hamayyar Arsenal a maimaikon ƙasar Rwanda.
Haɗin gwiwar ƙasar ta Afirka da ƙungiyoyin Arsenal da Bayern Munich da kuma Paris St-Germain na fuskantar suka daga ɓangarori da dama bayan rikici ya ɓarke a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda hukumomi suka ce an kashe mutane 7,000 tun daga watan Janairu zuwa yanzu.
Gwamnatin Congo dai na zargin Rwanda da bai wa ƴantawayen M23 makamai tare da tura dakaru domin tallafawa mayaƙan.
Duk da iƙirarin da Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka yi, Rwanda ta musanta cewa tana goyon bayan ƙungiyar.
Gunners for Peace ta ce, ƙuri'ar jin ra'ayinn jama'a da ta gudanar a baya bayan nan ya nua cewa shida cikin magoya bayan arsenal guda 10 sun goyi bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar da ke tsakanin kulob ɗin da ƙasar Rwanda.





