Zan bar APC idan aka sake zaɓar Abdullahi Abbas shugaban jam'iyyar - Ata

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ministan ma'aikatar gidaje da raya birane na Najeriya ya mayar wa shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas martani game da zargin da ya yi masa na cewa shi ba dan jam'iyyar ba ne.

Yusuf Abdullahi Ata ya ce yana nan daram akan bakarsa na yakar duk wasu kalamai da za su iya kai ga rashin nasarar jam'iyyar.

Ya shaidawa BBC shi cikakken dan jam'iyyar APC ne.

''Ba mu san sanda Ata ya zama ba dan jam'iyya ba , domin Ata bai ce ya bar jam'iyya ba, kuma jam'iyya tana da matakai na cewa ta kori mutum daga jam'iyya'', in ji shi

Ya kara da cewa shi da magoya bayansa ba su san 'wannene aka dauka' aka ce shi ba dan jam'iyya bane.

Ministan ya ce ya ji zargin da shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya yi kan cewa ya na yi wa jam'iyyarsu zagon kasa watau Anti- party kuma shi dan siyasar karamar hukuma ne amma ya yi ikirarincewa ya 'taka rawar gani a lokacin zabe wajan samar wa jam'iyyarsa da kuri'u'.

''Ai ni ina cin zabe a Fagge amma shi a Dala da mazabarsa ta Gwale , ka je ka duba ka gani kuri'a kusan dubu talatin ko hamsin aka ba APC, ni ko a nan Fagge mun ci kusan dubu goma sha takwas''

Ana dai ganin maganar da karamin ministan ya yi na cewa ba za su yadda da kalmomi da ake fada, wadanda kan iya tayar da hankali ko tunzura masu kada kuri'a a matsayin abinda ya janyo hayaniyya tsakaninsu.

Tun farko shugaban jam'iyyar na APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas ya nuna mamaki a kan abin da ya janyo maganar saboda lokacin zabe bai zo ba a cewarsa. Sai dai mininstan ya shaidawa BBC dalilin da yasa ya fadi haka.

''Abin da ya sa shine idan za ka yi tafiya, shiri ake fara yi , harkar nan duk wanda ya san za a yi zabe kasa da shekara biyu, sai kuma a ce kai ka yi shuru wanda yake jagorantarka yana tabo mutane kirki, kana tayar da hankali, masu zabe ba za su zabemu ba''

Ministan ya sake jadada cewa zai bar jam'yyar muddin aka tsayar da Abdullahi Abbas.

''Wallahi in aka mayar da shi, zan ajiye mukamin minista zan fita, domin mun san sai Allah ya kayar da jam'iyyar''

Game da anniyar shugaban jamiyyar APC na Kano na tsaya wa takarar gwamna sai ministan ya ce abu ne mai kyau amma ya bayar da shawara::

''Mu yanzu in ya fito ya ce yana takarar neman gwama, sai mu ce abu ya yi kyau, yana da yanci, yana da dama, ina bashi shawara idan yana son ya yi nasara to kada ya ce da tsiya-tsiya''. in ji shi.