Me ya sa matasa ke samun bugun zuciya da ƙananan shekaru?

    • Marubuci, Chloe Hughes
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, West Midlands
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A ranar 6 ga watan Janairun 2024, Faith Harrison ƴar kimanin shekara 22 a lokacin, ta fuskanci bugun zuciya a yayin da take tuƙa mota zuwa gida daga wani wasan ƙwallon sanda na hockey.

Bugun zuciyar ya kwantar da ita na tsawon sa'oi bakwai wanda ya kai ga yi mata tiyatar gaggawa, kuma likitoci suka gano tana da ciwon zuciya.

Watanni 12 bayan nan, a yanzu tana da shekara 23, rayuwar mai horas da masu motsa jikin da ke garin Shropshire na ƙasar Birtaniya ta sauya baki ɗaya.

''Ba ni kaɗai ba, har likitocina, sun bayyana ni a matsayin mai cike da lafiya, sai dai kuma suna ɗan mamakin cewa ina cikin ƙoshin lafiya, sosai,'' in ji ta.

''Idan na tuna baya, gaskiya na jahilci irin tsananin rashin lafiyan da nake ciki.''

Duk da ta sauya tsarin tafiyar da rayuwarta matuƙa, Ms Harrison na cigaba da fama da fargabar da ta shiga a lokacin da zuciyarta ta buga.

Ta bayyana jin takaici idan ta tuna rayuwar da take yi a baya.

''A wasu lokutan, ina jin ɓacin rai sosai, sai in ji kamar zan yi ihu in tambayi duniya: me ya sa sai ni?

''Wasu lokutan ina shiga tsananin ɓacin rai saboda ina tambayar kaina ya rayuwata za ta kasance inda hakan bai faru ba?''

Bayan zuciyarta ta buga, miss Harrison ta gano tana da cituttuka biyu da ba ta san da su ba tun haihuwa.

Tana da wani ciwo a zuciyarta mai suna 'patent foramen ovale' - wani ƙaramin rami a tsakanin ɓangarori biyu da ke saman zuciyarta.

Tana kuma fama da wani ciwo mai suna 'May-Thurner', wani ciwo da ba a cika gane shi ba, wanda ya fi shafar mata, wani yanayi da jijiyoyin da ke ɗauko jini daga zuciya suke dannne jijiyoyin da ke kai wa zuciya jini a ƙugu wanda hakan ke hana jini gudana yadda ya kamata.

Bayan likitoci sun gano tana da ciwon zuciya, sun faɗa mata cewa adadin jinin da ke fitowa daga zuciyarta duk lokacin da zuciyarta ta matse, kashi 27 ne cikin ɗari, wanda kuma kashi 50 zuwa sama ne ake ganin shi ne daidai.

''Ɓangarori 8 cikin 17 na zuciyata ba su aiki,'' in ji miss Harrison.

A yanzu, jinin da ke fitowa daga zuciyarta ya ƙaru zuwa kashi 47 bisa 100.

Da take tuna watanni 12 da suka gabata, ta ce : ''na yi nunki goma na abubuwan da ban yi tunanin zan yi ba.''

A yanzu ta zama jakadiyar wata gidauniyar kula da masu ciwon zuciya ta Birtaniya, kuma ta taimaka wajen wayar da kai kan matan da ke fama da ciwon zuciya.

''An yi min baiko, na zama malamar koyar da motsa jikin miƙe gaɓoɓi, na fara koyarwa, na kuma fara shirin rediyo (podcast) a yanar gizo... zan yi abubuwa masu yawa a shakarar 2025,'' kamar yadda ta shaida wa BBC.

Sai dai ta ce waɗannan nasarorin ba su zo ba sai da sadaukarwa.

"Dole sai da na sauya rayuwata baki ɗaya... a baya ina atisayen ɗaukar abubuwa masu nayi da kuma buga wasan ƙwallon hockey, amma yanzu na koma atisayen miƙe gaɓoɓi a kan tabarma, wannan bai kai wanda nake yi a baya ba.''

Ta kuma sauya irin abincin da take ci, a yanzu kuma tana shan magunguna da yawa a kullun, ciki har da magungunan hana dunƙulewar jini.

''Ba na ɗaukar komai da wasa, duk ƙanƙantar sa,'' a cewar ta.

''Iya hawa matakala, iya gyara gidana, da kuma iya yin atisaye.

''A gani na, iya yin hakan abin mamaki ne sosai saboda akwai mutane da dama da ke da irin wannan ciwon ko kuma suka yi fama da abin da na yi fama da shi, amma ba sa iya irin waɗannan abubuwan da nake yi.''

Miss Harrison ta ce tana fama da tuno abin da ya faru a baya.

''Akwai ranakun da nake jin ba na so na bar gida, kuma ina samun ciwo a ƙuguna, bugun zuciyata na ƙaruwa, ina zufa, sai in ji na tuno ranar farko da zuciyata ta buga,'' in ji ta.

A yayin da ake kusantar zagayowar ranar da ta samu bugun zuciya, Miss Harrison na alfahari da cigaban da ta samu.

''Na sa a yi min kek (cake),'' in ji ta.

''Babban kek mai siffar zuciya''

''Ina so in yi murnar samun dama ta biyu na yin rayuwa, ba rana ba ce da nake so in manta.''