Madrid na farautar Fernandes, City na son Pedri

Bruno Fernandes

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗanwasan Manchester United da Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 30, na cikin lissafin Real Madrid inda take shirin ware fam miliyan 90 domin ɗauko shi. (Star)

Sabon daraktan wasanni na Arsenal Andrea Berta na da ƙalubalen kammala yarjejeniyar ɗanwasan tsakiya na Spain da Real Sociedad Martin Zubimendi yayin da Real Madrid ta nuna sha'awar ɗanwasan. (Mirror)

Manchester City na ganin ɗanwasan tsakiya na Spain Pedri ya dace da tsakiyarta amma kuma Barcelona ba ta da burin sayar da ɗanwasan mai shekara 22. (Fichajes - in Spanish)

Manchester City ta tattauna kan ɗauko ɗanwasan Sweden mai shekara 20 Hugo Larsson, inda Eintracht Frankfurt ke son fam miliyan 50. (Sky Sports Germany)

Ɗanwasan baya na Barcelona Jules Kounde, na kan gaba cikin ƴanwasan da Chelsea ke farauta a bazara. (Sport - in Spanish, external)

Barca na dab da sabunta kwangilar golan Poland Wojciech Szczesny mai shekara 34 har zuwa Yunin 2026. (Fabrizio Romano)

Bournemouth na son ɗauko golan Spain Kepa Arrizabalaga daga Chelsea a wannan bazara. (Fabrizio Romano, external)

Atletico Madrid na son ɗanwasan tsakiya na Chelsea da Argentina midfielder Enzo Fernandez, mai shekara 24. (Fichajes - in Spanish, external)

RB Leipzig ta nuna matuƙar buƙatar ɗanwasan tsakiya na Sunderland Jobe Bellingham, mai shekara 19, amma ta nuna damuwa kan tsadarsa. (Sky Sport Germany, external)