Keane ya zama kocin Ferencvaros ta Hungary

Keane

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon kociyan Jamhuriyar Ireland, Robbie Keane ya zama mai horar da ƙungiyar Ferencvaros ta Hungary.

Keane, mai tarihin yawan ciwa Jamhuriyar Ireland ƙwallaye a tarihi, ya bar aikin jan ragamar Maccabi Tel Aviv a watan Yuni, bayan kaka ɗaya a ƙungiyar.

Tsohon ɗan wasan Tottenham da Liverpool ya ɗauki kofin Premier League a Israila da kai wa zagayen ƴan 16 a Europa Conference League.

Keane ya fara aikin horar da tamaula a 2018 a ATK ta India.

Ya kuma yi mataimakin kociyan Jamhuriyar Ireland da na ƙungiyar Middlesbrough da kuma Leeds United.

Mai shekara 44-ya maye gurbin Pascal Jansen, wanda ya karɓi aikin horar da New York City a makon jiya.

Ferencvaros tana ta biyu a babbar gasar tamaula ta Hungary, kuma ta 16 a wasannin zakarun Turai ta Europa League.