Man United na ɓalɓalcewa ƙarƙashin mulkin Ratcliffe - Cantona

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon tauraron ɗanwasan Manchester United Eric Cantona ya ce sabon mamallakin ƙungiyar Sir Jim Ratcliffe na rusa ta.
A watan Fabrairun 2024 ne kamfanin Ienos na Ratcliffe ya sayi kashi 27.7 cikin 100 na hannun jarin kulob din a kan fam biliyan 1.6.
Iyalan Glazer da ke da mafi yawan hannun jarin ƙungiyar ne ke ci gaba da mallakar ƙungiyar amma kuma Ineos ne yake jagorantar harkokin wasanninta.
A watan da ya gabata United ta bayyana shirinta na gina sabon filin wasa na kan fam biliyan biyu mai cin 'yankallo 100,000.
Ɗan Birtaniyan mai shekara 72 ya sha suka lokacin da ya ƙara farashin tikitin kallon wasan United, sannan ya kori ma'aikata karo biyu domin rage yawan kuɗin da suke kashewa.
Ratcliffe ya kare matakan da ya ɗauka yayin wata hira da BBC a watan Maris, yana mai cewa ƙungiyar "ta kusa talaucewa zuwa ƙarshen shekarar nan" ba don matakan da ya ɗauka ba.
"Tun da Ratcliffe ya zo ƙungiyar nan suke neman su lalata komai kuma ba su girmama kowa," a cewar tsohon ɗanwasan gaba Cantona, wanda ya buga mata wasa 185 daga 1992 zuwa 1997.
"Raina na ɓaci idan na ga United a cikin halin nan. Suna yanke hukunci kan abubuwa daban ta hanyar da suke so, wani aikin daban.
"Ina goyon bayan United saboda ina ƙaunar ta, amma da a ce ɗankallo ne ni kuma aka ce na zaɓi kulbo ba na jin zan zaɓi United."
Cantona da ya buga wa Faransa wasa 45 ya ce United "na da buƙatar ta gane gabanta" yayin da ya soki yadda aka cire Sir Alex Ferguson a matsayinsa na jakadan ƙungiyar na duniya.
"Ba shi son Sir Alex a matsayin jakada, amma ya fi ƙarfin tauraro [a United]," in ji Cantona.











