Jordan Henderson na daf da komawa Ajax

An wallafa

Tsohon dan kwallon tawagar Ingila, Jordan Henderson ya kusa komawa Ajax, bayan wata shida a gasar kwallon kafar Saudi Arabia a Al-Ettifaq.

An kammala tsara yadda za a yi masa tarbar girma a Amsterdam, amma har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba.

Mai shekara 33, ya saka hannun kan yarjejeniyar kaka uku a Al-Ettifaq kan £700,000 a kowanne mako, bayan da ya bar Liverpool a cikin Yulin 2023.

Wasu rahotanni na cewar baya jin dadin zama a Saudi Arabia, shi ya sa yake son komawa taka leda a nahiyar Turai.

Kocin Al-Ettifaq, Steven Gerrard ne ya dauki Henderson, wanda ya buga karawa 17 a babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia.

Tsohon dan kwallon Sunderland - wanda cikakken mai goyon bayan auren jinsi ne a lokacin da yake Anfield - ya sha caccaka, sakamakon amincewa da komawa buga kwallo Saudi Arabia, inda auren jinsi ke zama haramun.

Wasu magoya bayan Ingila sun yi wa Henderson ihu lokacin da ya buga wa Ingila wasa a wasan sada zumunta da Australia a Wembley cikin Oktoba.

Ajax na fuskantar kalubale a kakar bana, wadda take ta biyar a kan teburi da tazarar maki 23 tsakaninta da PSV Eindhoven ta daya.

Idan har za a kai ga cimma kwantiragi, Henderson ka iya fara wasa ranar Asabar a karawa da RKC Waalwijk a gasar kwallon Netherlands.