Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya za ta nemi shirya gasar cin kofin duniya ta 2034
Saudiyya ta tabbatar da aniyarta ta neman karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta 2034.
Hukumar kwallon kafa ta Saudiyya (SAFF) ta bayyana cewa ta na da niyyar shirya kasaitacciyar gasar cin kofin duniya karo na 25 tare da cewa yunkurin nata ya samo asali ne daga matukar sha'awar kwallon kafar da kasar ke yi.
Tuni dai aka tabbatar da kasar Saudiyya a matsayin kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin kwallon kafa ta shekarar 2023, da za a yi a birnin Jeddah a watan Disamba, da kuma gasar cin kofin nahiyar Asiya ta AFC ta 2027.
FIFA ta nemi a mika bukatar shirya gasar cin kofin duniya ta 2034 a ranar Laraba daga hukumar kwallon kafa ta Asiya da kuma hukumar kwallon kafa ta Oceania.
Hukumar kwallon kafa ta duniya ta kuma tabbatar da cewa Sifaniya da Portugal da Moroko sun shirya karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta maza ta 2030 - inda kasashe uku na kudancin Amurka suka shirya wasannin buɗe gasar don murnar cika shekaru ɗari da fara gasar.