Arsenal za ta yi rashin Gabriel Jesus saboda rauni

An wallafa

Ɗan wasan gaba na Arsenal Gabriel Jesus na iya yin jinya na 'yan makonni kaɗan bayan gwajin da aka yi masa ya tabbatar da rauni a ƙafarsa, in ji koci Mikel Arteta.

Jesus ne ya zura ƙwallo kuma ya taimaka aka ci yayin da Arsenal ta koma hanyar cin nasara a gasar zakarun Turai da ci 2-1 a Sevilla ranar Talata.

Sai dai ɗan wasan na Brazil mai shekaru 26 ya fice daga wasan bayan mintuna 81 sakamakon raunin da ya samu.

Shima ɗan wasan tsakiya Thomas Partey zai yi jinyar irin wannan lokaci.

An yi wa Jesus ƙaramar tiyata a gwiwa a watan Agusta kuma bai buga wasannin farko na gasar Premier ba.

Bayan da ya dawo cikin ƙoshin lafiya, ya fara buga wasanni huɗu da Arsenal ta fafata a baya-bayan nan, da kuma dukkan wasannin rukuni-rukuni na gasar zakarun Turai guda uku, inda ya zura ƙwallaye huɗu a kakar bana.

Arsenal wanda ba a doke ta a gasar Premier ba a bana, ta na mataki na uku a kan teburi, maki biyu a bayan Tottenham Hotspur da ke jan ragamar gasar a halin yanzu.