Brighton ta ɗauki Cozier-Duberr daga Arsenal

An wallafa

Brighton ta ɗauki Amario Cozier-Duberry, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Arsenal.

Mai shekara 19, wanda ya buga wa Gunners wasa daya, ya fara daga makarantar ƙungiyar tun daga Satumbar 2019.

Tuni ya amince da ƙunshin ƙwantiragin da Brighton ta gabatar masa, wadda za ta karkare a karshen 2028.

Arsenal ta yi wa Cozier-Duberry tayin tsawaita zamansa a Emirates a kakar da ta wuce, amma ya zaɓi ya bar ƙungiyar, wanda yarjejeniyarsa ya kare a karshen watan Yuni.

''Mun ji dadi da muka samu ɗaukar Amario,'' in ji dakartan tsare-tsaren Brighton, David Weir.