Reece James zai yi jinyar makonni

Reece James

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kyaftin din Chelsea Reece James na shirin yin jinya ta tsawon makwanni bayan ya samu rauni a kafarsa yayin gudanar da atisaye, in ji koci Mauricio Pochettino.

Dan wasan mai shekaru 23 ya fara yunkurin murmurewa bayan likitoci sun tantance yanayin raunin.

James ya fara wasan da Chelsea ta buga da Liverpool a Stamford Bridge a ranar Lahadin da ta gabata, kafin daga bisani aka sauya shi a minti na 77.

Wannan dai ba karamin ci baya ba ne ga dan wasan na Ingila, wanda ya buga wasanni 16 ne kacal a gasar Premier a kakar wasan da ta wuce sakamakon fama da rauni.

James ya samu rauni a gwiwarsa a watan Oktoba wanda hakan ya sa bai buga wa Ingila gasar cin kofin duniya ta 2022 ba, kafin daga bisani ya yi jinyar karin makwanni hudu sakamakon raunin da ya samu a wasansa na farko a watan Disamba.

James, wanda ya taso daga sashen matasan Chelsea kafin ya fara taka leda a shekarar 2019 bayan ya dawo daga aro a Wigan, ya zama kyaftin din kungiyar a wannan bazarar bayan tafiyar Cesar Azpilicueta.