Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ghana ta kara yi wa Najeriya fancalen shiga gasar CHAN
Tawagar Najeriya da ta Afirka ta Kudu ba za ta shiga gasar kofin nahiyar Afirka ta 'yan wasan da ke taka leda a nahiyar da za a yi a Algeria da ake kira CHAN ba.
Sai dai a karon farko Madagascar za ta samu shiga gasar wadda za a yi a 2023.
Ghana ce ta yi waje da Najeria a bugun fenariti, bayan da suka tashi 2-2, ita kuwa Afirka ta Kudu ta sha kashi da ci 4-1 a hannun Angola, jumulla 6-1 gida da waje.
Madagascar wadda ita ce kadai bakuwa a wasannin da za a kara nan gaba ta yi 1-1 da Botswana a Antananarivo ranar Juma'a, amma ta kai bantenta da ci 2-1 gida da waje.
Kawo yanzu an samu kasashe bakwai da za su buga CHAN karo na bakwai tun lokacin da aka kirkiro gasar da suka hada da mai rike da kofin Morocco da Kamaru da Jamhuriyar Congo da Ivory Coast da kuma Senegal.
Tuni dai mai rike da kofin Morocco da mai masaukin baki Algeria da Libiya suka samu gurbin buga gasar, bayan da Masar da Tunisia suka janye daga wasannin Arewacin nahiyar.
Gasar ta CHAN da aka kara ta zuwa kasashe 18 jumulla, za a fara tsakanin 13 ga watan Janairu zuwa 4 ga watan Fabrairun 2023.
Za a raba jadawalin wasannin a Algeria ranar 1 ga watan Oktoba.
Ghana ce ta hana Najeriya zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.
Tawagogin da za su buga CHAN 2023:
Algeria (Mai masaukin baki), Morocco, Libya, Senegal, Mauritania, Mali, Niger, Ghana, Ivory Coast, DR Congo, Congo, Cameroon, Sudan, Ethiopia, Uganda, Madagascar, Angola, Mozambique.
Sakamakon wasannin zagaye na biyu, karawa ta biyu
Yammacin Afirka A
Guinea 1-0 Senegal (1-1 agg - Senegal win 5-3 on pens)
Mali 2-0 Sierra Leone (4-1 agg)
Mauritania 1-0 Guinea-Bissau (2-0 agg)
Yammacin Afirka B
Burkina Faso 0-0 Ivory Coast (0-0 agg - Ivory Coast win 5-3 on pens)
Niger 3-1 Togo (3-2 agg)
Nigeria 2-0 Ghana (2-2 agg - Ghana win 5-4 on pens)
Shiyyar Afirka ta tsakiya
Congo 1-0 Central African Republic (2-2 agg - Congo win on away goals)
Cameroon 2-0 Equatorial Guinea (2-1 agg)
DR Congo 5-0 Chad (7-1 agg)
Tsakiyar gabashin Afirka
Rwanda 0-1 Ethiopia (0-1 agg)
Uganda 3-0 Tanzania (4-0 agg)
Sudan 3-2 Djibouti (7-3 agg)
Shiyyar Kudancin Afirka
South Africa 1-4 Angola (1-6 agg)
Madagascar 1-1 Botswana (2-1 agg)
Mozambique 0-0 Malawi (1-1 agg - Mozambique win on away goals)