Uefa za ta binciki Barcelona kan sayen wasanni

An wallafa

Uefa za ta yi bincike kan Barcelona, sakamakon kudin da ta biya tsohon mataimakin shugaban kwamitin rafli a Sifaniya.

Tuni hukumar ta nada jami'in da zai yi bincike kan kudin da ake zargin Barcelona ta yi don ta samu sakamakon wasannin da zai amfane ta.

An shigar da karar Barcelona kan tuhumar cin hanci da bayar da rahoton karya da aikata rashin gaskiya.

Masu shigar da kara na tuhumar Barcelona da biyan fam miliyan 7.1 ga Jose Maria Enrique Negreira da kamfaninsa Dasnil 95.

Barcelona wadda ta musanta aikata ba daidai ba ta ce ta biya kudin ga Dasnil 95 tsakanin 2001 zuwa 2018.

Uefa ta ce: "Ta nada jami'in da zai binciko ko Barcelona ta karya dotar hukumar kan kudin da ake zargin ta biya Caso Negreira.''

Wani gidan rediyo ne mai suna Ser Catalunya ya bayar da rahoton biyan kudin daga nan mahutuntan karbar haraji suka fara bibiyar Dasnil 95.

"Barcelona ta cimma yarjejeniyar baka da baka a boye da Jose Maria Enriquez Negreira a matakinsa na mataimakin kwamitin alkalan tamaula a Sifaniya da biyansa kudi domin kungiyar ta amfana da samakon wasanni,'' in ji masu shigar da kara a Sifaniya.

Barcelona ta ce ta biyan kudin ne domin a hada mata rahoto a faifan bidiyo kan yadda alkalan ke gudanar da aikinsu, kamar yadda kociyoyonta suka bukata, don taimaka musu wajen gudanar da aiki.

Wadanda ake tuhuma sun hada da tsohon shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu da Sandro Rosell da kuma Negreira.

Ofishin masu shigar da kara ne ya kai batun kotu, domin a tuhumi Barcelona.

Shugaban gasar La Liga, Javier Tebas ya ce ya kamata shugaban Barcelona na yanzu, Joan Laporta ya yi murabus idan ya kasa bayani kan wannan tuhumar.

Real Madrid ta ce tana goyon bayan a tuhumi Barcelona, sannan a shirye take ta bayar da sheda a gaban kotu, domin ta kare martabar ta.