Mbappe zai bar PSG a bana

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe ya shaida wa PSG aniyarsa ta barin ƙungiyar a ƙarshen kakar bana.

Dan wasan mai shekara 25 kwantaraginsa za ta ƙare da PSG a ƙarshen wannan kakar, kuma ana ta yaɗa jita-jitar Real Madrid zai koma.

Sanin makomarsa kan zai tafi ko ba zai tafi ba ya zamarwa ƙungiyar ƙarfen ƙafa a wannan kakar.

A baya, sai da aka cire Mbappe daga tawagar farko ta PSG, ta kuma ajiye shi ba ta je wasannin share fagen kaka da shi ba wanda ta yi a Asia.

Daga baya aka cimma yarjejeniya saboda kada ƙungiyar ta yi asara lokacin da zai tafi kuma har yanzu babu wanda zai fada maka sharuɗan da aka sanya na tafiyar shi.

Dan wasan gaban yana da damar tsawata zamansa a ƙungiyar da shekara guda, shi ya sa aka riƙa hasashen cinikinsa zai kasance ko dai sai an biya kuɗaɗen tsarabe-tsarabe ko kuma ɗan wasan ya yi hakuri da wasu kudade masu yawa.

PSG za ta so ɗan Mbappe ya ci gaba da zama a ƙungiyar, fitarsa na zuwa ne lokacin da ake tsaka da gina tawagar yara, sannan kuma a daina sayan manyan ‘yan kwallo, wanda wannan ne ya sa Messi da Neymar suka bar ƙungiyar a bara.

An yi hasashen Mbappe na ɗaukar yuro miliyan 200 a shekara.

A baya, yana sane yaƙi haɗuwa da wakilan ƙungiyar Al-Hilal daga gasar Saudi, kuma tayin da aka yi masa ya haura duk wani kuɗi da aka sayi wani ɗan kwallo a duniya fan miliyan 259.

Daga baya ɗan wasan ya koma tawagar farko ta PSG bayan doguwar tattaunawa da shugabannin ƙungiyar.

Mbappe ya yi watsi da tayin da Real Madrid suka yi masa lokacin da ya yarda ya ci gaba da zama a PSG a watan Mayun 2022.