Man United na son Terland, Arsenal na daf da siyan Merino

An wallafa

Liverpool na tattaunawa don siyan dan wasan baya na Crystal Palace Marc Guehi, Adam Wharton yana son ci gaba da zama a Selhurst Park, yayin da Arsenal da Aston Villa ke fafatawa kan Mikel Merino, da sauran su.

Liverpool na neman Marc Guehi, kuma tuni ta fara tattaunawa don siyan dan wasan na Crystal Palace da Ingila mai shekara 24. (Fabrizio Romano})

Dan wasan tsakiya na Ingila Adam Wharton, mai shekara 20, zai ki amincewa da bukatar Manchester City, da Bayern Munich da Real Madrid don ci gaba da zama a Crystal Palace. (Sun)

Arsenal ta cimma yarjejeniya kan siyan matashin golan Ingila Tommy Setford, mai shekara 18, daga Ajax. (Athletic)

Wolves ce ke kan gaba wajen neman dan wasan bayan Sheffield United Anel Ahmedhodzic, mai shekara 25, a kan fam miliyan 20, don maye gurbin Max Kilman dan Ingila mai shekara 27, wanda ya koma West Ham. (Sun)

Arsenal ce ke kan gaba, kuma tana shirin doke Aston Villa a fafatukar sayen dan wasan tsakiya na Real Sociedad da Spain Mikel Merino, mai shekara 28, a bazarar nan. (Mundo Deportivo)

Manchester City za ta tattauna da dan wasanta na Argentina Julian Alvarez, mai shekara 24, bayan kammala gasar Copa America. Paris St-Germain na sha'awar dan wasan wanda ke son karin lokacin buga wasa, amma City na son ci gaba da rike shi. (Fabrizio Romano)

Manchester United na shirin dauko dan wasan gaban Norway Elisabeth Terland, mai shekara 23 daga Brighton. (Guardian)

Za a bar Jakub Kiwior ya bar Arsenal a bazara kuma dan wasan bayan na Poland mai shekaru 24 yana jan hankalin kungiyoyin Seria A da dama. (Football Insider)

Liverpool na son dan wasan bayan Sporting Lisbon da Portugal Goncalo Inacio, mai shekara 22 (CaughtOffside)

Juventus na zawarcin dan wasan tsakiyar Atalanta dan kasar Holland Teun Koopmeiners, mai shekara 26, wanda shi ma Liverpool ke zawarcinsa. (Rudy Galetti)