Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutumin da ya sha kaye sau biyar da mutanen da suka yi nasara karon farko a zaben Kenya
Kenya ta gudanar da ɗaya daga cikin zaɓuka mafi taƙaddama tun bayan da aka kawo ƙarshen mulkin Jam'iyya guda a 1991 yayin da ƴan takara ke ta neman muƙamai.
A nan mun yi nazari kan waɗanda suka yi nasara da waɗanda suka sha kaye, a ƙoƙarinsu na neman mulki.
1) Ɗan takarar da ya fi shan kaye
Raila Odinga, mai shekara 77, shi ne ɗan takarar shugaban Kenya da ya fi shan kaye a ƙasar. Ya tsaya takarar shugaban ƙasa sau biyar kuma duk ya sha kaye inda ya ce maguɗi aka tafka.
Kotun Kolin Kenya ta wanke shi bayan zaɓen 2017 lokacin da ta soke zaben da ya bai wa Shugaba Uhuru Kenyatta nasara tare da umartar a sake gudanar da zaɓen.
Mista Odinga ya ƙaurace wa zaɓen da aka sake gudanarwa inda ya ce ba a tsara shi bisa gaskiya da adalci ba.
Da alama a shirye yake ya sake zuwa kotu bayan da ya yi watsi da nasarar da Mataimakin Shugaban Ƙasar William Ruto ya samu a zaɓen ranar 9 ga watan Agusta inda ya lashe zaɓen da fiye da kashi 50 cikin 100.
Ƙarar ta Mista Odinga ta sake ƙarfi kasancewar huɗu daga cikin Kwamishinonin zaɓe bakwai - har da mataimakiyar shugabar hukumar, Juliana Cherera - sun yi fatali da sakamakon zaɓen.
Ms Cherera ta ce zaɓen cike yake da kura-kurai kuma idan aka duba alƙaluman da Shugaban hukumar zaɓen, Wafula Chebukati ya sanar - adadin ya zarce kashi 100.
Amma masu sharhi sun ce wannan kuskure ne wajen tattara alƙaluma - kuma sun amince da sakamakon zaɓen da Mista Chebukati ya sanar.
A karon farko hukumar ta bai wa kafafen yada labarai da ƙungiyoyin farar hula damar tattara alƙaluman zaɓen, domin tabbatar da gaskiya.
Ana ɗora sakamakon zaɓe daga mazaɓu a shafin intanet na hukumar. Sannan ƙungiyoyin da ke sa ido a zaɓen cikinsu har da ƙungiyoyin farar hula sun goyi bayan Mista Chebukati inda suka ce ƙirgen da suka yi ya yi dai-dai da sakamakon ƙarshe na hukumar sannan tsarin bayyana sakamakon ya yi armashi.
Amma idan ya zaɓi zuwa kotu, ko Mista Odinga zai yi nasara karo na biyu a kotun ko kuma zai sake fuskantar koma-baya?
Za mu san haka da zarar Kotun Kolin ta saurari ƙarar, ta kuma yanke hukunci.
Zuwa yanzu, Mista Ruto - wanda ya lashe zabe karon farko da ya nemi takarar -shi ne zaɓaɓɓen shugaban kasa duk da cewa za a samu tsaiko wajen sauyawa daga gwamnati Shugaba Ukuru Kenyatta idan har kotu za ta yanke hukunci.
A lokacin yaƙin zaɓe, Mista Kenyatta ya bayyana Mista Ruto a matsayin wanda ba shi da amana inda ya goyi bayan takarar Mista Odinga don ya gaje shi.
Tun bayan da aka sanar da sakamakon zaɓen dai Mista Kenyatta bai ce uffan ba yayin da kwamitin miƙa mulki ya gabatar da jawabi kwana uku kafin a sanar da sakamakon zaɓe.
Kwamitin ya ce zai fara shirye-shiryen miƙa mulki da zarar hukumar ta sanar da mutumin da ya yi nasara a zaɓen amma ba ta ce komai ba tun bayan da taƙaddama ta ɓarke.
Shugaban ƙasa da mataimakinsa ne mutanen da suka fi iko a siyasar Kenya amma dangantakarsu ta yi tsami tun bayan da Mista Kenyatta ya daidaita da Mista Odinga a 2018.
Akasarin ƴan Kenya na fatan mutanen biyu za su yi aiki tare a maimakon kitsa rikici - idan aka ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu.
Sakamakon zaɓen ko kaɗan bai yi wa magoya bayan Mista Odinga daɗi ba saboda ana ganinsa a matsayin Jigon Dimokraɗiyya kasancewar yana gaba-gaba a kamfe ɗin bai wa wasu jam'iyyu dama, sai kawai Fadar Shugaban ƙasa ta jingine shi a gefe.
2) Matan da suka kafa tarihi
An samu gagarumin ci gaba kan shigar mata harkokin siyasa a Kenya inda aka zaɓi mata bakwai a matsayin gwamnoni.
Wannan ya bambanta da zaɓen 2017 inda aka zaɓi mata uku.
Gwamnoni ke riƙe da maƙudan kuɗaɗen jihohi kuma ana sa ran za su jaragamar samar da ayyukan ci gaba a yankunansu.
Matan sun yi fatali da tsangwama da cin zarafi da wariya wajen samun nasara. Sun haɗa da Wavinya Ndeti wadda ta zama mace ta farko da ta zama gwamna a Machakos bayan ta yi nasara kan maza uku.
Ms Ndeti na auren wani ɗan asalin Najeriya mazaunin Birtaniya - marigayi Dolamu Henry Oduwole, wanda ta haɗu da shi a lokacin da take karatu a London.
Masu suka na mata kallon baƙuwa saboda ta auri baƙo amma ta dage cewa ita ƴa ce ga Machakos.
Amma matar da ta ja hankalin galibin al'ummar kenya ita ce Linet Chepkorir mai shekara 24.
Za ta zama matashiya ta farko a zauren majalisar dokokin ƙasar bayan nasarar da ta yi ta neman wakiltar al'ummar gundunar Bomet.
Ms Chepkorir ya faɗa wa BBC cewa wannan ne aikinta na farko. "Ina son na ƙarfafa wa masu tasowa gwiwar cewa komai mai yiwuwa ne," a cewarta.
Babu tabbaci kan ko an samu ƙari a yawan matan da ake damawa da su a majalisar dokoki kasnacewar hukumar zabe ba ta fitar da jerin ƴan majalisar da suka yi nasara ba.
Abin da muka sani shi ne al'ummar Kenya sun gaza tsayar da mace ta farko a matsayin mataimakiyar Shugaban Ƙasa sakamakon shan kaye ga kuma taƙaddamar zaɓe tsakanin Mista Odinga da abokiyar takararsa, tsohuwar Ministar Shari'a Martha Karua.
Ta zama mai kamala a lokacin yaƙin neman zaɓe, ba ta cika caccakar abokan hamayyar ta ba amma ta gaza samarwa Mista Odinga ƙuri'u .
Mista Ruto ya lallasa Mista Odinga a mazaɓarta abin da ya sa masu amfani da shafukan sada zumunta suke jefa mata kalaman nuna wariya.
"Tana wakiltar kayan da take sawa ne kawai." kamar yadda wani ya faɗa. Saƙon ya nuna cewa duk da ci gaban da aka samu wajen kare haƙƙin mata a Kenya, da alama akwai sauran rina a kaba a yaƙi da kalaman wariya.
3) Mai neman sayar da wiwi da dafin maciji
George Wajackoyah, mutumin da ya taso cikin gwagwarmaya, daga baya ya zama Farfesa a fannin Lauya, ya fita daban cikin jerin ƴan takarar shugaban ƙasa.
Ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya kuma ja hankalin dubban jama'a - musamman matasa - a yaƙin zaɓe inda ya yi alƙawarin haɓaka tattalin zarkin ƙasar ta hanyar mayar da ƙasar zama babbar mai samar wa da fitar da tabar wiwi da dafin maciji da kuma marenan kura.
Ƙuri'un jin ra'ayi sun yi hasashen zai lashe kashi biyar cikin 100 na ƙuri'un da aka jefa da ƙyar ya samu ƙasa da kashi daya na ƙuri'un.
David Waihiga lauya ne kuma rabaran wanda ya samu kashi 0.23 cikin 100. Rashin nasarar tasa ba ta zo da mamaki ba. Ya yi alƙawarin yaƙi da cin hanci amma ya gaza samar da sauyi.
Kasancewar duka ƴan takarar biyu sun gaza samun kashi ɗaya cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa, ya nuna ƙarara cewa lokacin da lamarin ya zo, sai al'ummar Kenya suka mayar da zaɓinsu tsakanin Mista Ruto da Mista Odinga.
Sun san cewa idan har suka zaɓi Shugaban ƙasar da ba shi da rinjaye, hakan zai kara ba da damar sake zaɓe, wani abu da suke ƙoƙarin kaucewa.
4) Ɗan takara mai wankin bandaki ya sha kaye
Wani ɗan siyasar wanda ya riƙa bai wa al'ummar Kenya nishadi lokacin yakin zaɓe shi ne Polycarp Igathe wanda ya nemi takarar kujerar gwamnan Nairobi.
Ya wanke bayi, ya wanke motoci, ya kuma yi aiki a kantin sayar da abinci da nishadantar da abokan hulɗa a lokacin da yake ƙoƙarin gamsar da masu zaɓe cewa a shirye yake ya ja ragama.
Sai dai ya sha kaye a hannun Johnson Sakaja, wanda sam ba ya shakkar jan hakalin jama'a, ya wallafa hotunansa yana sayen kifi a bakin titi da yadda yake sayen tumatur da albasa a kasuwa a maimakon a kanti.
Mista Sakaja shi ne Sanata mai wakiltar Nairobi kafin ya samu mukamin gwmana.
Didmus Barasa, shi ma ɗan majalisar da ke wakiltar Kimilili ne da ya samu nasara, wanda ya yi amfani da murhu wajen haɗa wa wata mata ƴar shekara 67 da mai gidanta ya mutu shayi, yana sanye da talakma masu tsada yayin da yake yakin zaɓe.
Mista Barasa, wanda mazaɓarsa ke Yammacin Kenya, a yanzu yana hannun ƴan sanda zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zargin harbi da kashe mataimakin abokin hamayyarsa bayan wata sa-in-sa da ta faru a wata mazaɓa a ranar zaɓen.
Ɗan majalisar, a lokacin da ya miƙa wuya ga ƴan sanda, ya ce yana son sanin abin da ya faru ga matashin da aka kashe.
Tsohon Sanata Boni Khalwale shi ma ya lashe zaɓe a ƙoƙarinsa na neman a sake tsayar da shi a matsayin Sanata na gundunar Kakamega a Yammacin Kenya.
Yayin zaɓe, ya zaɓi wanke takalmi a gefen titi sannan ya ci gasashshiyar masara yayin da yake jiran a wanke masa su.
A yanzu, ƴan Kenya na jiran su ga ko shi da sauran waɗanda suka lashe zaɓe za su manta da ƙalubalen al'ummarsu - ko kuma samar da shugabanci na gari.