Putin ya ce Rasha ta kai hare-haren makamai masu linzami 83 Ukraine

An wallafa

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tabbatar da cewa ƙasarsa ta kai hare-haren makamai masu linzami a wasu sassan ƙasar Ukraine da safiyar Litinin

A wani jawabi da ya yi a bidiyo, ya ce makamai masu linzamin masu dogon zango sun samu wasu cibiyoyin makamashi da sadarwa da kuma na soji.

Putin ya yi alkawarin mayar da "mummunan martani" ga duk wani "ta'addanci" a kan iyakar Rasha.

Ana sa ran a ranar Litin 10 ga watan Oktoba shugaban na Rasha zai gana da kwamitin tsaro na ƙasarsa don tattauna batun harin bam da ya tayar da gadar da ta haɗa Rasha da Crimea - inda ya dora alhakin hakan a kan Ukraine.

Hare-hare 83 aka kai

Da safiyar yau Litinin ne aka wayi gari Rasha ta kai hare-hare da dama a manyan biranen Ukraine.

Ga dai jerin hare-haren da muka san an kai zuwa yanzu:

  • A ƙalla an harba makamai masu linzami 83, kamar yadda shugaban rundunar sojin Ukraine ya ce
  • A ƙalla fararen huka takwas ne suka mutu sannan 24 sun jikkata sakamakon harin makami mai linzami da aka kai babbabn birnin Ukraine, Kyiv, a wani lamari da ba a saba kai wa ba, a cewar wani mataimaki na musamman ga ministan harkokin cikin gida. Mahajin garin birnin ya ce harin ya shafi manyan wurare masu muhimmanci
  • Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya kuma ce an kai wasu hare-haren Dnipro- da Zaporizhzhia - yana mai cewa Rasha "na son kawar da mu ne daga doron ƙasa"
  • Magajin birnin Kharkiv ya ce makamai masu linzami sun faɗa kan wata cibiyar makamashi, inda hakan ya jawo ɗaukewar lantarki
  • Kazalika an harba makamai masu linzamin Ternopil da Lvivin a yammacin, kamar yadda jami'ai a dukkan yankunan suka ce.
  • Magajin garin Lviv - da ke yammacin birnin inda yaƙin bai taɓa munana a can ba, ya ce a yanzu babu wuta a mafi yawan birnin
  • Rahotanni sun ce bama-bamai sun tashi a yankunan Sumy da Zhytomyr da Khmelnytskyi da Kirovohrad.

Shugabannin Turai sun yi Allah-wadai da RAsha

Tuni ƙasashen Turai suka fara mayar da martani kan lamarin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kira wani taron gaggawa da takwarnsa na Ukraine Volodymyr Zelensky.

Macron ya jaddada goyon bayansa ga Ukraine ya kuma nuna damuwa kan asarar rayukan fararen hula da aka samu, a cewar wata sanarwa daga Fadar Elysée Palace.

Shugaba gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi magana da Zelensky, yana mai tabbatar masa da goyon bayan Jamus da sauran ƙasashe bakwai mafiya ƙarfin tattalin arziki na duniya, kamar yadda mai magana da gwamnatin Jamus ya faɗa.

Ministan harkokin wajen Poland Zbigniew Rau ya ce hare-haren makamai masu linzamin laifukan yaƙi ne", yana mai cewa "Rasha ba za ta yi galaba a yaƙin nan ba. Muna bayanku Ukraine!"

Ministan harkokin wajen Birtaniya James Cleverly shi ma ya yi Allah-wadai da lamarin, yana cewa ba za a yarda da hare-haren Rasha a kan fararen hula ba, kuma hakan nuna gazawar Shugaba Vladimir Putin ne".