Manyan gasar Turai za ta kai Fifa kara

Europa League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manyan gasar tamaula ta Turai har da Premier League da ƙungiyar ƴan wasa ta duniya za su ɗauki matakin shari'a kan Fifa da cewar ''yin kama karya a fannin tamaula.''

Gasar Turan mai wakilcin gasa 39 da ƙungiyoyi 1,130 daga kasa 33 ta ce za ta shigar da korafi ga hukumar Turai, domin ta kai Fifa kotu, saboda a kare hakkin ƴan wasanta.

Hakan ya biyo bayan matsin da ya karu daga lik da ƴan wasa da ƙungiyar ƙwararrun ƴan wasa kan yawan wasannin da aka kara a kalanda, wanda ke shafar lafiyar ƴan ƙwallo.

Ƙungiyar ƴan wasan ta fitar da jawabin cewar kalandar da Fifa ta tsara ''ta zarta kima'' kuma "mara dorewa ga wasannin kasa" da "hadari ga lafiyar 'yan wasa".

Gasar Turai ta hada da ta Ingila da ta Scotaland da ta ƙwararrun ƴan wasa da ta Serie A da Bundesliga. Sai dai babu ta La Liga, wadda yanzu ke fatan zama mamba.

A cikin watan Mayu Fifa ta yi watsi da ikirarin cewa ba a tuntubi ƙungiyar ƴan wasa ba da ƙungiyar gasa lik ta duniya kan shirin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya mai ɗauke da kungiyoyi 32.

Manchester City da Chelsea suna cikin ƙungiyoyin Turai 12 da za su wakilce ta a sabuwar gasar Club World Cup, wadda aka sauya fasali da karin ƙungoyi da za a yi a Amurka tsakanin 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yulin 2025.