Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Watakila Maguire ya buga wa United wasa da FC Sheriff
Harry Maguire ya koma atisaye, watakila ya buga wa Manchester United gasar Europa League da za ta fafata da Sheriff Tiraspol ranar Alhamis.
Mai tsaron bayan tawagar Ingila, mai shekara 29 baya buga wasanni tun bayan raunin da ya ji a lokacin da ya yi wa kasarsa tamaula a cikin watan Satumba.
Takwaransa Raphael Varane zai yi jinya zuwa bayan gasar kofin duniya, bayan da ya ji rauni a wasan Premier League da United ta tashi 1-1 da Chelsea a Stamford Bridge a karshen mako.
Haka shima Donny van de Beek da Aaron Wan-Bissaka sun murmure sun kuma koma atisaye.
Kocin United, Erik ten Hag ya sanar cewar Cristiano Ronaldo ya koma cikin sauran ‘yan wasan kungiyar, bayan da aka ajiye shi a karawa da Chelsea.
Kyaftin din tawagar Portugal ya ki ya shiga fili ya canji dan wasa, bayan da aka umarce shi a lokacin da yake zaman benci a fafatawa da Tottenham.
Rabon da Maguire ya yi wa United tamaula tun wasan da kungiyar ta je ta ci FC Sheriff 2-0 ranar 15 ga watan Satumba.
Magoya bayan tawagar Ingila da na United sun yi wa Maguire ihu a bana, shi ne ya tafka kuskuren da aka ci Ingila kwallo biyu a wasan da ta tashi 3-3 da Jamus ranar 26 ga watan Satumba.