Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dage wa'adin ranar yin tayin sayen Man United
Mai kamfanin Ineos, Sir Jim Ratcliffe da mai banki a Qatar, Sheikh Jassim za su sake yin tayin sayen Manchester United.
Tun farko an tsayar da ranar Laraba, domin yin tayin karshe, sai aka samu takaddamar da aka kara wa'adin.
An sanar da masu zawarcin sayen United da su sake mika tayin kafin karfe 21:00 agogon GMT.
An sanar da BBC Sport wasu da dama sun mika tayin da suka sake yi don sayen United tun kan wa'adin ya cika.
Sai dai ba a fayyace ranar da aka tsayar ta wa'adin karshe ba ta nan gaba.
Ratcliffe da Sheikh Jassim, sune kadai suka sanar da cewar sun taya United da kudi mai tsoka.
An kuma sa ran a yammacin Laraba za su mika sabon tayin a kan wanda suka yi a baya.
Kuma tun kan wa'adin suka mika bukatar a kara musu lokaci, domin shiri na biyu wajen yin tayin ga Raine - bankin hannun jari da yake da alhakin sayar da United - wanda ya amince da bukatar
Sai kuma aka ji cewar an kara wa'adi kan Laraba da aka tsayar tun farko.
To sai dai wasu na hangen watakila iyalan Glazer su canja shawara kan sayar da kungiyar Old Trafford.
Ineos na son sayen hannun jarin iyalan Glazer da ya kai kaso 69 cikin 100, shi kuwa Sheikh Jassim so yake ya sayi kaso 100 cikin 100 na United.