Gabriel ya fara buga wa Brazil wasa a karon farko

An wallafa

Dan kwallon Arsenal, Gabriel ya fara buga wa Brazil tamaula a karon farko ranar Juma'a a wasan neman shiga gasar kofin duniya.

Brazil ta caskara Bolivia 5-1 a wasannin neman buga gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Canada da Mexico.

Tun daga Nuwambar 2021 da kuma Janairun 2022 aka gayyaci dan kwallon Arsenal, amma sai a ranar Juma'a ya fara buga wa Brazil wasa.

Koci Fernando Diniz ya saka Gabriel a matakin mai tsaron baya tare da dan kwallon Paris Saint-Germain Marquinhos.

Gabriel ya buga minti 84 daga baya aka canje shi, bayan da Rodrygo ya ci kwallo biyu da Raphinha ya zura daya a raga, sannan Neymar ya kara biyu.

Neymar, wanda ya ci biyu a wasan ya haura tarihin Pele da kwallo 79 a raga a matkin kan gaba a ci wa Brazil kwallaye a tarihi.

A minti na 79 ne, Victor Abrego ya zare kwallo daya daga biyar da aka zura a ragar Bolivia.

Gabriel Jesus ya shiga wasan karo na 60 kenan da ya buga wa Brazil tamaula, yayin da daya dan kwallon Arsenal, Gabriel Martinelli ya yi zaman benci.

Ranar Talata Brazil za ta kara da Peru a Lima a dai wasan na neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026.