Barca ta kara cin Real karo na biyu a jere a El Clasico

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Barcelona a wasan farko a daf da karshe a Copa del Rey da suka buga a Santiago Bernabeu.
Barcelona ta yi nasara bayan da Real Madrid ta ci gida ta hannun Eder Militao a minti na 26.
Wannan shi ne karo na uku da suka fafata a tsakaninsu a bana, Real ta ci Barcelona 3-1 a La Liga a Santiago Bernabeu ranar 16 ga watan Oktoba.
Sai dai Barca ta doke Real Madrid 3-1 ranar 15 ga watan Janairu ta lashe Sifanish Super Cup a Saudi Arabia.
Barcelona ta buga wasan ne, bayan da Manchester United ta fitar da ita daga Europa League da cin 4-3 gida da waje.
Haka kuma kungiyar Nou Camp ta yi rashin nasara a hannun Almeria a La Liga a karshen mako, karo na biyu da ta yi rashin nasara a gasar a kakar nan.
Ita kuwa Real Madrid ta tashi 1-1 a wasan hamayya da Atletico Madrid a dai fafatawar hamayya a babbbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Barcelona ce ta daya a teburin La Liga da tazarar maki bakwai tsakaninta da Real Madrid ta biyu.
Ranar 19 ga watan Maris, Barcelona za ta karbi bakuncin Real Madrid a fafatawar La Liga.
Real Madrid za ta kara ziyartar Barcelona a wasa na biyu a Copa del Rey fafatawar daf da karshe ranar 5 ga watan Afirilu a Camp Nou.
Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31, Real Madrid 19 ne da ita, wadda ke biye da Athletic Bilbao mai 23.
Ranar 5 ga watan Maris Real Madrid za ta ziyarci Real Betis domin buga karawar La Liga a kuma ranar Barcelona za ta karbi bakuncin Valencia.










