Chiellini ya yi ritaya daga taka leda

Giorgio Chiellini

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Fitatcen dan kwallon tawagar Italiya, Giorgio Chiellini ya sanar da yin ritaya daga taka leda.

Mai shekara 39, wanda shi ne kyaftin din Italiya a Euro 2020 ya daina sana'ar tamaula bayan shekara 23.

Mai tsaron bayan ya yi suna a Juventus, wanda tun daga 2022 ke taka leda a gasar kwallon kafar Amurka, Major League Soccer a Los Angeles.

Ranar Asabar Columbus Crew ta doke Los Angeles 2-1 a wasan makon karshe a gasar kwallon kafar Amurka.

Chiellini ya fara taka leda yana matashi a Livorno a 2000, wanda daga baya ya zama fitatcen dan wasa a gasar Serie A a kungiyar birnin Turin.

Ya lashe Serie A tara a jere a Juventus tsakanin 2011 zuwa 2020 da kuma Copa Italia biyar.

Tsohon kyaftin din Italiya, wanda ya yi ritaya daga buga wa kasarsa tamaula a 2022, ya ci mata kwallo takwas a wasa 117.