Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce ya yarda da iya kwallon Maguire
Kocin Manchester United Erik ten Hag yace ya yarda da kwallon kyaftin din kungiyar Harry Maguire duk da sukar da ake yi wa dan kwallon.
Maguire na shan suka daga magoya bayan kungiyar tare da magoya bayan kasarsa bayan kuskuren da ya tafka a wasansu da Jamus a wasan da suka yi 3-3 a Nations League.
“Ina kare shi saboda na yarda kuma na amince da shi” in ji Erik.
“Maganar dai a kan shi ce, kuma na yi imani cewa zai iya abin da duk muke bukata, zai dawo kokarinsa kamar yadda yake a baya, ni na yarda da haka”.
Ten Hag ya fi sanya Lisandro Martinez da kuma Raphael Varane a matsayin yan bayansa da yake sanyawa, yayin da yake bai wa Bruno Fernandez kyaftin a yan makonnin nan.
Wasa uku kacal Maguire ya bugawa Manchester United a wannan kakar.
“Duk da cewa baya cikin 11 tawagarmu na farko amma yana atisaye sosai, Ten Hag ke cewa kan dan wasan me shekara 29.
“Abin da ya fi mahimmanci shi ne,kwarewarsa tana nan, ya bugawa ingila wasa sama da 50 haka Leicester da Manchester United.”
A wannan makon takwaransa na Ingila da Manchester United Luke Show yace “bai taba ganin irin sukar da ake yi wa Maguire ba a tahirin kwallon kafa.”
Maguire ba zai buga karawar da Manchester United za ta yi ba da abokiyar hamayyarta Manchester City ba a ranar Lahadi saboda raunin da ya ji