Kalvin Phillips ba zai buga wa Ingila Nations League ba

Kalvin Phillips

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan kwallon Manchester City, Kalvin Phillips ba zai buga wa tawagar Ingila Nations League karawa da Italiya da Jamus ba, sakamakon rauni a kafada.

Phillips baya cikin 'yan kwallon da City' ta doke Wolves 3-0 a gasar Premier League ranar Asabar.

Koda yake ya buga fafatawar da City ta yi nasara a kan Borussia Dortmund 2-1 a Champions League ranar Laraba, wanda ya shiga daga baya.

City ba ta yanke shawarar ko za a yi wa Phillips tiyata ba, hakan zai zama baraza ga dan wasan mai shekara 26, watakila ya kasa zuwa Gasar Kofin Duniya a bana a Qatar.

Tun bayan da dan kwallon ya koma Etihad daga Leeds a bana kan £45m ya shiga wasa sau uku a matakin canji, jumulla minti 14 ya yi.

Dan kwallon yana daga cikin wanda kociyan Ingila, Gareth Southgate ya kare, bayan da aka bukaci ya fayyace yadda ya zabo 'yan wasan da ya sanar. ranar Alhamis.

Saura mako tara kafin Ingila ta fara wasan farko a cikin rukuni a Gasar Kofin Duniya ranar 21 ga watan Nuwamba a Qatar.