Alisson Becker na daf da komawa tsare ragar Liverpool

An wallafa

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce mai tsaron ragar kungiyar Alisson Becker na daf da komawa buga wa kungiyar wasanni.

Ya kuma ce dan kwallon tawagar Brazil, ba zai tsare ragar kungiyar ba a wasan sada zumunta da za ta yi ranar Laraba da Salzburg, sakamakon jinya.

Rabon da Alisson ya kama gola tun bayan 4-0 da Manchester United ta doke Liverpool a Bangkok mako biyu da suka wuce.

Liverpool za ta buga wasan sada zumunta da Salzburg a cigaba da shirye-shiryen da take na tunkarar kakar da za a fara ta bana a cikin watan Agusta.

Ranar Asabar Liverpool za ta buga Community Shield da Manchester City a filin wasa na Leicester City, wato King Power.

Ana buga Community Shield tsakanin wadda ta lashe Premier League a kakar da ta wuce da wadda ta dauki FA Cup - daga nan a fara Premier League ta kakar.

Liverpool ce ta yi ta biyu a kakar da aka kammala a Prenier League ta kuma lashe FA da League Cup, ita kuwa City ta yi nasarar daukar babban kofin gasar tamaula ta Ingila a ranar karshe.