Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Na san za a iya kama ni a kowane lokaci' - Rayuwar ƴan Afirka a Amurka
'Yan cirani na cikin 'zaman ɗarɗar' a Amurka musamman ga waɗanda da ba su da cikakkun takardun izinin zama. ''Abin da muke fuskanta tamkar farauta ce,'' cewar Beaugard, wani ɗan cirani da ya shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba da ke zaune a jihar Ohio.
Yanzu haka yana cikin tashin hankali game da halin da 'yan'uwansa ke ciki, waɗanda aka tilasta wa barin gidajensu bayan da jami'an shige da fice suka kai musu samame.
Tun bayan komawarsa fadar White House a ranar 20 ga watan Janairun da ya gabata, sabon shugaban ƙasar, Donald Trump ya alƙawarta aiwatar da alƙawuransa na yaƙin neman zaɓe, musamman kan korar 'yan ci ranin da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.
'Da dama cikin abokaina da na sani a wasu jihohin tuni sun dakatar da zuwa ayyukansu. Saboda a nan ne ake kama su ,'' a cewar Ousmane (ba sunansa na gaskiya ba), wani ɗan Senegal mai cirani da ya je Amurka ba bisa ƙa'ida, wanda kuma ke zaune a wata jiha da ke arewacin Amurka, kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Ya ƙara da cewa 'yan ciranin da ba su da takardu a yankin kudancin ƙasar a yanzu na cikin kaffa-kaffa, saboda gwamnan jihar ba ya tare da manufofin Donald Trump.
To amma Ousmane na sane cewa yana fuskantar barazanar fitar da shi daga Amurka.
''Ko ma dai mene ne mun san ba mu tsira ba''.
Yana cikin matuƙar damuwa, musamman da ya ji cewa ana ci gaba da kama mutane tare da fitar da su daga manyan jihohi kamar su Chicago da Atlanta da California da New York da sauransu.
''Suna kama mutane a wuraren sana'o'insu tare da mayar da su ƙasashensu ba tare da komai ba, ba su da lokacin ɗaukar ko sisi cikin kuɗinsu ko kuma zare cikin tufafinsu,'' kamar yadda Beaugard ya ya ƙarin haske.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya alƙawarta ''gagarumar korar baƙi a tarihin Amurka'', lamarin da zai shafi dubban mutane da ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.
A ranar 23 ga watan Janairu, kakakin fadar White House, Karoline Leavitt ta bayar da rahoton cewa jami'an hukumar shige da fice sun kama 'yan cirani 538 da suka shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba, tare da mayar da ɗaruruwansu ƙasashensu ta hanyar amfani da jiragen soji.
A cewarta, mutanen ''masu laifi ne da suka shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba'', ciki har da waɗanda ake yi wa zargin ta'addanci da waɗanda ake zargi da laifukan fyaɗe kan ƙananan yara da sauran laifuka.''
Halin ƙunci da fargaba da 'yancirani marasa takardu ke ciki
Manyan ƙalubalen da aka fuskanta dangane da dokokin shige da fice sun faru ne bayan dawowar Donald Trump wa'adin mulki na biyu.
Gwanatin Trump ta tsaurara dokokin shige-da -fice ba bisa ƙa'ida ba, kamar yadda Annick Attorney Koloko, wata babbar lauya, kuma mamba a ƙungiyar lauyoyin ta New York, ta bayyana wa BBC.
Lamarin da ta ce yana haifar da fargaba tsakanin 'yan gudun hijira da 'yanciranin da ba su da cikakkun takardu waɗanda ke fuskantar kora.
"'Yan cirani na cikin fargaba, inda har wasu suka janye yaransu daga makarantu, yayin da wasu kuma suka tare a gidajensu, ba sa zuwa ko sayayya,'' in ji ta.
Ousmane, wanda ke zaune a ƙasar ba bisa ƙa'ida ba na kusan shekara biyu da rabi, ya ce yana cikin barazana, duk da iƙirarin da ya yi na cewa yana zuwa aiki, tare da ci gaba da gudanar da harkokinsa, saboda ƙarancin fargabar da ake da ita a jihar da yake zaune.
"Ba za mu zauna a gida mu kasa yin komai ba. Rayuwa na da muhimmanci. Muna da iyalai a Senegal da dole sai mun taimake su. Amma dole mu yi taka-tsantsan saboda shiga matsalar da za ta sa a fitar da mu.''
A jihar da yake zaune a arewacin Amurka, Ousmane na da damar zuwa wurin aikinsa.
"Amma magana ta gaskiya akwai wannan fargabar, cewa za su iya zuwa har inda kake domin kama ka tare da fitar da kai ba tare da komai naka ba, wannan shi ne abin da ke razana ni,'' in ji shi.
Gujegujen ƴan cirani daga jiha zuwa jiha
Yayin da suke cikin mawuyacin hali, ko'ina ka duba za ka ga mutane, musamman 'yan Afirka a cikin wani yanayi na rashin ƙa'ida, suna yin ƙaura daga jiha zuwa jiha, musamman wuraren da ba kasafai ake kamen ba.
Wannan kaura ta 'yancirani marasa takardun izini ta fi yawa a jihohin Chicago da California da Atlanta da New York da Ohio, da sauransu.
''Waɗannan jihohi, biranensu na maƙare da 'yancirani, don haka yanzu suke ƙoƙarin ficewa'' a cewar Ousmane, wanda ya ce yana da abokai waɗanda suka fice daga irin waɗannan birane domin komawa wuraren da babu barazana.
Ya ƙara da cewa, wasu daga cikin abokansu, sun yanke shawarar ficewa daga Amurka, domin komawa Canada. To sai dai ya ce ko can ma a Canadar za su zauna ne ba bisa ƙaida ba.
"Ina da abokai a nan da ba sa son komawa Senegal ko Afirka. Saboda sun kashe miliyoyin kuɗi kafin su zo nan, kuma kawo yanzu ba su mayar da kuɗin da suka kashe ba. Na san wanda ya kashe miliyan shida kafin ya zo nan, kuma har yanzu yake fafutika.''
A yanzu duka irin waɗannan mutane na fargabar zuwa aiki, musamman waɗanda ke da matsala da dokokin ƙasar.
Kuma abu ne mai wahala mutum ya zauna ba tare da aikin yi ba, ko don cikinsa ma. A gefe guda kuma ga fargabar kame.
"Akwai wani abokina da ya faɗa min cewa a makon da ya gabata bai je wurin aikinsa ba, amma jami'an shige da fice sun je kamfanin da yake aikin, inda suka kama mutane masu yawa, galibi 'yan Mexico, lamarin da ya sa ya dakatar da zuwa aikin. Tabbas wannan abu yana damun mu,'' a cewar Ousmane.
Haka kuma ya bayyana cewar akwai hatsari game da ƙaurar da ake yi daga jiha zuwa jiha. Abokansa sun shaida mana cewa sun shafe tsawon kwanaki ba tare da ganin 'yan'uwansu ba, saboda sun tafi wata jihar.
Da dama daga cikin waɗannan 'yan cirani sun haƙura da ayyukansu da zuwa sayayya da masallatai da sauran wurare saboda jami'an shige da fice.
Ousmane ya jaddada cewa a jihar da yake akwai kwanciyar hankali, saboda yadda gwamnan jihar ke adawa da matakin korar baƙi na Donald Trump.
Mutanen da korar baƙin ta shafa
"Ƙaramar matsala sai ta janyo maka kora daga ƙasar," cewar Ousmane, wanda ya ce dole sai mutum yana taka-tsantsan saboda kada jami'ai su kama shi.
A cewar Me Annick Koloko "mutanen da ake hari a kamen, su ne waɗanda aka kama da manyan laifuka da waɗanda aka bai wa umarnin ficewa daga ƙasar''.
Mutanen da suka shiga ƙasar ta hanyar tekun Nicaragua su ne aka fi nema. 'Yansanda na bibiyarsu, saboda ''ba su da cikakkun takardun izinin aiki a ƙasar'', a cewar Ousmane.
Akwai zaɓin da ya rage wa marasa takardun izini?
Me Annick Koloko ta tsaya wa 'yan cirani da dama a kotunan Amurka.
Duk da hukuncin korar da hukumomin Amurka suka yi, Ms Koloko na iya ɗaukaka ƙara zuwa wasu kotunan tare da tabbatar da hakkokin da suke da shi.
A wannan yanayin, dole ne ɗan cirani ya kasance ba shi da wani laifi da aka taɓa kama shi da shi a baya.
Don haka akwai hanyoyin ɗaukaka ƙara ga waɗanda ke da damar samun kariya daga korar tasu.
Hukumar shige da ficen Amurka na ɗaukar ma'aurata masu shaidar zama 'yan Amurka, a matsayin 'yan'uwan juna da za su iya samun biza saboda su.
''Daɗin daɗawa, mutanen da ke zaune a Amurka na tsawon shekara 10 ka iya buƙatar soke korarsu
"Bugu da ƙari, mutanen da suka yi shekara 10 a Amurka suna iya neman a soke tsarin korar da aka yi musu, idan hakan zai shafi matansu na Amurka ko 'ya'yansu da ke da izinin zama na dindindin a ƙasar," in ji Me Koloko.
A ƙarshe, su ma mutanen da wani kamfani ya ɗauki nauyinsu suna iya ƙalubalantar korarsu a kotunan ƙasar.
"Muna taimaka wa waɗanda muke wakilta. Muna wakiltarsu su a gaban kotunan shige da fice, da kuma a gaban hukumar USCIS. Muna kuma taimaka wa abokan hulɗa da ke son daidaita matsayinsu daga 'yan gudun hijura zuwa baƙi," in ji lauyan.
Ousmane na shirin fara harkar noma a ƙasarsa ta Senegal. ''Ba mu da shirin zama a Amurka na har abada. Ina fatan wata rana na koma Senegal domin rayuwa cikin 'yan'uwa da dangi, mun yi karatu, ina da digiri na biyu, kuma muna da aniyar hidimta wa ƙasarmu. Mun zo nan ne domin samun rayuwa mai inganci. Amma matsawar abubuwa ba su daidaita ba, muka riƙa shan wahala, to gwara mu koma ƙasarmu, mu nemi wani abin yi.''
Dangane da abin da ya ce mana, yana da gona a Niayes (Senegal), inda yake shirin noma kayan lambu.