Ladubban tafiya Idin Babbar Sallah

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A yau Juma' ne al'ummar Musulmi a faɗin duniya, ke gudanar da Idin Babbar Sallah na shekarar 1446 bayan hijira, daidai da 2025.

Sallar Idi ibada ce da Allah (SWT) Ya shar'anta a matsayin ibadu na shekara-shekara, da ake yi sau biyu a cikin kowace shekara, wato Idin ƙaramar Sallah da kuma na Babbar Sallah.

Sheikh Idris Yunus, malamin addinin Musulunci a Najeriya ya ce Idin Babbar Sallah, babbar rana ce ta biki a Musulunci, da ake son musulmi su gudanar da raha da farin ciki da jin daɗi.

''Rana ce ta alkairi da abubuwa na alkari ke yawo, cikin sabbin tufafi da kai-komon abinci da sauransu'', in ji shi.

Ibadar na ɗaya daga cikin sunnoni masu ƙarfi a addinin Musulunci, wadda ta ƙunshi fita zuwa masallaci domin yin salla raka'a biyu, haɗe kabarbari.

Don haka ne ma sallar idin ke buƙatar wasu abubuwa domin yin guzuri a tafiya zuwa masallacin idin.

Dakta Muhammad Nazifi Inuwa wani malamin addini ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ya bayyana jerin abubuwan da ya kamata mutum ya yi kafin tafiya sallar idi.

Za ku iya samun ƙarin labaran addini a tasharmu ta WhatAspp. Ku shiga ta a nan

Wankan Idi

Wankan Idi ɗaya ne daga cikin wanka na sunnah a addinin Musulunci wanda ake yi sau biyu a shekara.

''Yana da kyau kowane mutum ya yi wankan idi kafin tafiya sallar idi,'' a cewar malamin.

Dangane da wankan, Dakta Nazifi ya ce mutum zai iya yin wanka na soso da sabulu domin tsaftace jikinsa, sannan daga baya kuma sai ya yi wankan idin, domin dacewa da ladan sunnar wankan.

Haka kuma malamin ya ce sigar wankan iri ɗaya ne da na sauran wankan addinin Muslunci, kamar na janaba, da na ɗaukewar jinin al'ada ko na biƙi, sai dai kawai niyya ce ta bambanta.

Tsaftace jiki

Malamin ya ce tsafta na daga cikin ladubban addinin Musulunci, don haka kasancewar ranar Idi rana ce ta musamman, yana da kyau mutum ya ƙara tsaftace jikinsa.

''An so mutum ya tsaftace jikinsa ta yadda zai je masallaci ba tare da ya cutar da masallata, da warin jikinsa ba''.

Yawaita kabarbari

Dakta Nazifi ya ce ana so mai tafiya masallaci ya ci gaba da kabarbari.

Malamin ya ce ya zo a cikin ruwayoyi masu yawa na irin kabarbarin da za a riƙa yi sun haɗa da:.

''Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha illallah Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamdu'', Malamin ya ce haka mutum zai riƙa fada, kuma da sauti mai ƙarfi ta yadda zai jiyar da na kusa da shi.

Malamin ya ce hikimar yin kabarbarin cikin sauti mai ƙarfi shi ne don tunatar da waɗanda suka manta da yin kabarbarin.

Dakta Nazifi ya kuma koka kan abin da ya ce wasu matasa ke yi a lokacin tafiya masallacin idin, inda ya ce sai ka ga wasu matasan sun shagalta da hirarrakin duniya a kan hanyarsu ta tafiya masallacin idin.

'Ba a nafila gabanin sallar Idi'

Sheikh Idris Yunus ya ce idan mutum ya isa masallacin Idi, abin da ake son ya yi shi ne ya zauna jiran ƙarasowar liman, tare da ci gaba da kabarbari.

''Ba a yin sallar nafila gabanin sallar Idi don haka abin da ake son mutum ya yi shi ne ya zauna jiran isowar liman, ya kuma ci gaba da kabarbari'', in ji malamin.

Ya ƙara da cewa ''da zarar liman ya iso masallaci babu abin da zai yi kawai sai tayar da sallah ba tare da ɓata lokaci ba.

Haka kuma ana so a zauna a saurari hudubar liman, bayan kammala sallar, ba a son daga sallame sallah a fice daga masallaci don tafiya gida.

Jinkirta cin abinci ga masu layya

An so masu yanka dabbar layya ya jinkirta cin abinci gabanin sallar idi, har zuwa bayan sallar idi bayan ya yanka dabbarsa.

''An so mutum ya fara cin wani abu daga cikin dabbar da ya yanka, kamar hanta ko wani ɓangare na kayan ciki'', a cewar Sheikh Idris.

Wannan ya saɓa da sallar idin ƙaramar sallah, inda ake son mutum ya fara cin abinci gabanin tafiya sallar idin.

A jira liman ya yanka dabba kafin kowa

An so masu yanka dabbobin layya su jinkirta har zuwa saukowa daga sallar idi, bayan Liman ya yanka ragonsa.

Manzon Allah S.A.W ya ce: ''Duk wanda ya dabbarsa kafin liman, to ya ci nama ne kawai ba layya ba'', a cewar Sheikh Idris Yunus.

Sheikh Idris Yunus ya bayyana dabbobin da ake so a yanka domin ibadar layya da suka haɗa da raƙumu shanu da awaki ta tumaki

Malamin addinin ya kuma ce an fi so kowa ya yanka dabbarsa da kansa, mace ko maniji kowa zai iya yanka, kuma za a iya wakilta wani ya yi, kamar yadda Sheikh Idris ya yi ƙarin haske.

''Yanka na dabbar layya, ba a taƙaita shi ga maza kawai ba, har da mata su ma za su iya yi, abin da kawai ake so shi ne mace ta cire tsoro ta yanka dabbarta bayan yin addu'ar ''Bismillahi Allah Akbar''.